Mutane 5000 Ke Neman Shiga Aikin Hisbah a Kano, In Ji Hukumar Hisbah

Mutane 5000 Ke Neman Shiga Aikin Hisbah a Kano, In Ji Hukumar Hisbah

- Mutane fiye da 5000 ne ke neman shiga aiki a Hukumar Hisbah ta jihar Kano

- Harun Ibn Sina, shugaban hukumar ne ya sanar da hakan yayin taron karshen wata

- Ibn Sina ya ce hukumar ta bada umurnin fara ɗaukan sabbin jami'a saboda muhimmancinsu ga al'umma

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce fiye da mutane 5000 ne suka aike ta takardun neman aiki a matsayin jami'an Hisbah a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar da kakakin hukumar, Lawal Ibrahim ya fitar a ranar Laraba a Kano, ya ce Shugaba Hukumar, Harun Ibn Sina ne ya sanar da hakan a taron karshen wata na hukumar.

Mutane 5000 Ke Neman Shiga Aikin Hisbah a Kano, In Ji Hukumar Hisbah
Mutane 5000 Ke Neman Shiga Aikin Hisbah a Kano, In Ji Hukumar Hisbah. Hoto: @daily_nigerian
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Ibn Sina ya ce an bada umurnin fara ɗaukan sabbin jami'an hukumar a dukkan masallatai saboda muhimmanci su a gari.

"Za a fara aikin ɗaukan sabbin jami'an a hedkwatar hukumar a kananan hukumomi 44 da ke jihar tuni kuma anyi nisa wurin tuntubar kwamitin jihar na allurar-rigakafin Covid-19.

"Kazalika, an ɓullo ta tarukan kara wa juna ilimi ga jami'an domin inganta ayyukan su a fadin jihar," in ji shi.

KU KARANTA: 2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC

Ya gargadi jami'an hukumar da su guji aikata duk wani abu da zai bata sunan hukumar da kyakkyawar alakar ta da mutane.

Ibn Sina ya shawarci su da su rika shiga da ta dace da dokar aikinsu kuma mata su rika saka hijabi da niƙabi.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel