Majalisa: Sata za ayi, hankali ba zai dauka ba, ace an kashe $1.5bn wajen yi wa matata faci

Majalisa: Sata za ayi, hankali ba zai dauka ba, ace an kashe $1.5bn wajen yi wa matata faci

- ‘Yan Majalisa sun yi fatali da shirin gyara matatar Fatakwal a kan $1.5bn

- Bangaren marasa rinjaye sun ce wannan dabarar sace kudin gwamnati ne

- Ndudi Elumelu ya ce ba su goyon-bayan hakan, ya ce a dai sake duba aikin

Majalisar wakilan tarayya ta nuna adawar ta ga shirin da ake yi na kashe Dala $1.5bn wajen gyara matatan danyen mai da ke garin Fatakwal.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, bangaren marasa rinjaye a majalisar tarayyar su na ganin an lafta kudi, an yi sama da farashin kwangilar.

Ndudi Elumelu a madadin ‘yan majalisa masu hamayya sun bukaci a sake duba kudin kwangilar.

Honarabul Ndudi Elumelu ya fitar da jawabi, ya ce sun fitar da jawabi ne bayan sun zauna, sun yi nazarin wannan aikin da gwamnati za ta yi.

KU KARANTA: Atiku ya soki shirin kashe $1.5bn don gyaran matatar mai

An yi wa jawabin ta ke da: “Bangaren marasa rinjaye a majalisar wakilai sun nemi a duba $1.5bn matsayin kudin aikin gyaran matatar Fatakwal.”

‘Ya ‘yan hamayyar sun ce binciken kudin aikin da aka yi ya nuna katuwar badakala ce kurum wasu miyagun mutane su ka tsara da sunan gyaran.

A cewarsu, an dauko wannan aiki ne da nufin sace kudin gwamnati, ‘yan majalisar su ka ce za a iya yin wannan aiki a kudin da ba su kai haka ba.

‘Yan majalisar wakilan sun ce su na goyon bayan duk wani kokari da ake yi na magance matsalar mai, amma ba ta goyon-bayan a saci kudin jama’a.

Majalisa: Sata za ayi, hankali ba zai dauka ba, ace an kashe $1.5bn wajen yi wa matata faci
'Yan majalisar wakilai a zaure
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An yi alkawarin yi wa matatar man da ke jihar Ribas kwaskwarima

“Wannan makudan kudi $1.5bn da aka ware, ya nuna danyen aikin da wasu marasa kishi su ke shirin yi na wawurar baitul-mali.” inji Elumelu.

Hon. Elumelu ya ce: “Ana neman karkatar da kudi ta hanyar tada kudin kwangila saboda son-kai.” Ya ce kwakwalwa ba za ta dauki wannan ba.

Tun a baya kun ji cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na cigaba da shan suka a kan yunkurin kashe tulin kudi wajen gyaran matatar mai.

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana adawarsu da rashin jin dadi game da shirin da gwamnatin tarayya na kashe zunzurutun kudi a wannan aikin.

Source: Legit.ng

Online view pixel