Muna kan bakanmu, ba zamu taba yarda a sa Hijabi a makarantunmu ba, Cocin Katolika

Muna kan bakanmu, ba zamu taba yarda a sa Hijabi a makarantunmu ba, Cocin Katolika

- Duk da hukuncin kotu da umarnin gwamna, Kiristoci a Kwara sun ki amincewa dalibai mata su sanya hijabi a makarantun Mission

- Gwamnatin Jihar ta bayyana makarantun na ta ne, ba na coci ba

- Kungiyar lauyoyi Musulmai MULAN ta ce kungiyar CAN rikici kawai take nema

Shugaban Cocin Katolikan Ilori, kuma shugaban kungiyar Kirisotcin Najeriya shiyar Kwara, Most Rev. Paul Olawoore, ya ce cocin bata shiga wani yarjejeniya da gwamnatin jihar kan amincewa da sanya Hijabi a makarantun Mission ba.

Ya caccaki gwamnatin jihar kan kokarin da take yi na kwace makarantun daga hannunsu.

Yace, "Ba na son wani fito-na-fito da zai haddasa rikici da raunata wani. Kuma ba zan so wani ya rasa rayuwarsa kan wannan lamari ba."

Malamin ya kara da cewa lokaci ya yi da ya kamata su hada kai wajen nuna cewa zaman lafiya ne mafita ga kowa.

DUBA NAN: Dalilin da yasa sararin samaniyar masallacin Ka'aba ya zama ja jazur

Muna kan bakanmu, ba zamu taba yarda a sa Hijabi a makarantunmu ba, Cocin Katolika
Muna kan bakanmu, ba zamu taba yarda a sa Hijabi a makarantunmu ba, Cocin Katolika
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fayemi: Duk da cewa ni gwamna ne, 'yan sanda sun sha kai min hari

Diraktan hada kan coci-coci na kungiyar CAN, Rev. Fr. Ralph Ajewole, ya yi watsi da rahotannin cewa Kiristocin jihar sun amince da sanya Hijabi a makarantunsu.

Ya ce duk karerayi ne kuma ba zasu taba yarda ba

"Muna jaddada cewa cocin Katolika ba za ta amince da sanya Hijabi a makarantun Mission ba, " yace.

"Duk yadda akayi kokarin juya maganar, muna tare da CAN cewa ba zamu amince da sanya Hijabi a makarantun da Kiristoci suka gina ba."

A bangare guda, Shugaban cocin Winners Chapel, Bishop David Oyedepo, ya shawarci Musulmai da su bar makarantun mishan na Kwara ga masu su.

Ya ce ya kamata su nemi makarantun da ake sanya hijabi da yaransu za su iya zuwa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a cikin watan Fabrairu ne gwamnatin jihar Kwara ta rufe makarantu 10 a kan rikicin sanya hijabi (suturar Musulunci) ta dalibai mata musulmai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng