'Yan Bindiga Sun Sace Faston Cocin Katolika Da Mai Girkinsa a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Faston Cocin Katolika Da Mai Girkinsa a Kaduna

- Ƴan bindiga sun sace faston cocin katolika da wasu mutane a daren ranar Litinin Kaduna

- Joseph Hayab, shugaban kungiyar kirista ta CAN, reshen jihar Kaduna ya tabbatar da lamarin

- Hayab ya ce an sace faston ne tare da wasu mutane a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Kachia

Yan bindiga sun sace, Mista Anthony Dawah, Faston Cocin Katolika, mai masa girki, da matar wani mai koyar da sabbin wadanda suka karbi addinin kirista ibada a ƙauyen Kushe Makaranta a ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 2 na daren ranar Litinin a lokacin da ƴan bindigan suka kai hari a garin, rahoton The Cable.

An Sace Faston Cocin Katolika Da Mai Dafa Masa Abinci a Kaduna
An Sace Faston Cocin Katolika Da Mai Dafa Masa Abinci a Kaduna. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

Lamarin na zuwa ne bayan kwanaki takwas da sace mambobin cocin RCCG takwas a ranar Juma'a a hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Mista Joseph Hayab, shugaban Kungiyar Kiristocin Nigeria ta CAN a jihar ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin.

"An sace Reverend Fada Dawah misalin ƙarfe 2 na daren Litinin tare da mai masa girki da matar mai koyar da sabbin wadanda suka karbi addinin kirista da wasu mutane," in ji Hayab.

"Har yanzu yana hannun yan bindigan kuma ba su kira sun faɗa inda suke ba," ya ƙara da cewa.

KU KARANTA: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Muhammad Jalige, kakakin rundunar yan sandan jihar bai ɗaga wayansa ba a lokacin da aka kira shi.

A wani labarin daban, kun ji cewa 'yan bindiga sun bindige tsohon shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Tafa ta jihar Niger, Ishaya Sule, sun kuma yi awon gaba da matarsa mai suna Rebecca.

Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya ce lamarin ya faru a daren ranar Lahadi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce yan bindigan sun afka gidan mamacin da ke Bwari-Saba a karamar hukumar Tafa misalin karfe 1.22 na daren ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel