Yanzu-yanzu: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

Yanzu-yanzu: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya

- Watanni bayan gargadi kan rijistan layukan waya da yawa, ministan sadarwa ya dau mataki

- Dakta Isa Fantami ya umurci hukumar NCC dake karkashinsa ta sanar da kamfanonin sadarwa shawarar da ya yanke

- Ya ce duk kamfanin da bai bi ba zai rasa lasisin aiki a Najeriya

Hukumar sadarwan Najeriya, ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa su dakatad da rijistan sabbin layukan waya a fadin tarayya.

NCC ta bayyana hakan ne a jawabin da diraktan yada labaranta, Dr. Ikechukwu Adinde, ya saki ranar Laraba.

Jawabin yace hukumar ta bada umurnin haka ne bisa ga manufar gwamnatin tarayya na duba rumbun wadanda sukayi rijista da kuma tabbatar da cewa kamfanonin na bin ka'idoji da sharruda.

Ta ce ya zama wajibi a dakatad da layukan wayan da ba'ayi rijista ba wajen ayyukan banza.

KU DUBA: An rantsar Farfesa Mahmoud Yakubu matsayin shugaban hukumar INEC

Yanzu-yanzu: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya
Yanzu-yanzu: Dr Isa Pantami ya yi umurnin dakatad da sayar da sabbin layukan waya Credit: @thecableng
Source: Twitter

A cewar jawabin: "Bisa ga manufar gwamnatin tarayya na cigaba da samun nasara wajen rijistan layukan waya, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, ya umurci hukumar ta kaddamar da binciken rumbun rijista."

"Manufar wannan bincike shine tabbatar da cewa an bin ka'idoji da sharrudan da aka gindayawa kamfanonin sadarwa."

"Wannan umurni na da muhimmanci saboda yawaitan layukan waya da ba'ayi rijista ba kuma ake amfani da su wajen ayyukan laifi."

"Saboda haka, ana umurtan kamfanonin sadarwa su dakatad da sayar da sabbin layuka da rijista har sai an kammala bincike."

"Za'a kwace lasisin duk kamfanin sadarwan da bai bi wannan umurni ba."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisa, Munguno

Watanni goma da suka gabata mun kawo muku cewa ministan sadarwa, Dakta Isa ali Pantami, ya umurci hukumar sadarwan Najeriya NCC ta tabbatar da cewa kada kowani dan Najeriya ya mallaki fiye da layukan waya 3.

Ministan ya bada umurnin ne a ranar Laraba a jawabin da hadimin, Dakta Femi Adeluyi, ya rattaba hannu inda ya umurci NCC ta sake duba dokar rijistan layukan waya.

Jawabin ya kara da cewa akwai bukatan hakan ne bisa ga rahoton da aka samu daga hukumomin tsaro, bayan samun nasarar kawar layukan da ba'ayi rijista ba a Satumban 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel