An sha ni, na warke: Dalilin da ya sa na daina ba mata mukamai yanzu inji Ministan Buhari

An sha ni, na warke: Dalilin da ya sa na daina ba mata mukamai yanzu inji Ministan Buhari

- Ministan Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce ya daina ba mata mukami yanzu

- Rotimi Amaechi ya ce ana zargin mutum da neman mace idan ya bata aiki

- Ministan ya ke cewa akwai bukatar mata su hau kujeru domin sun fi basira

Babban ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Chibuike Amaechi, ya ce ya daina ba mata mukamai saboda irin abin da su ke yi idan su ka samu labari.

Ministan ya yi wannan bayani ne wajen taron kungiyar ‘yan kasuwa mata watau Association of Nigerian Women Business Network (ANWBN) a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Rotimi C. Amaechi ya na cewa mata matsala ne a kan karon kansu.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin cigaba da tallafawa mata a Najeriya

Ministan ya koka da cewa a Najeriya duk lokacin da aka ba mace kujerar matsayi, sai mutane su rika cewa mutum ya na soyayya da ita ne, ba wai ta dace ba.

A cewar Ministan sufurin, da zarar an ga mace ta na rike da mukami ko wani babban ofis, jama’a su kan ce ba domin ta cancanta ta samu matsayin ba.

Amma duk da haka tsohon gwamnan na jihar Ribas ya na ganin cewa ya kamata mata su rika samun mukamai fiye da maza, saboda sun fi maza kaifin basira.

Ba na goyon-bayan maza su danne kowa, ba kuma na goyon bayan mata su danne kowa.” Ministan ya ce ya fi yarda da a dauko duk wanda ya cancanta.

KU KARANTA: Amaechi ya yi magana a kan wanda zai gaji Buhari a 2023

An sha ni, na warke: Dalilin da ya sa na daina ba mata mukamai yanzu inji Ministan Buhari
Rotimi Amaechi da Mai dakinsa Judith Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Rotimi Amaechi ya yi wannan jawabi ne ta bakin hadimarsa, Taiye Elebiyo-Edeni a karshen makon jiya.

“Ban yarda cewa a ajiye wata kujera a gefe da sunan ta mata ba; dalilin kuwa shi ne mata sun fi maza kaifin kwakwalwa nesa ba kusa ba.” Inji Ministan.

Amaechi ya ce babu dalilin da idan an zo taro za a ga mata su na tika rawa, maimakon su yi wani abin kirki, ya yi kira ga mata su shiga siyasa a rika yi da su.

A ranar Litinin ku ka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ba mutane biyar mukamin darektoci a ma'aikatar ASENI, daga ciki akwai wasu mata biyu.

Sanarwar ta fito ne a lokacin da aka ji Shugaban kasar zai tafi kasar waje yau. Darektocin da aka nada sun hada da Olayinka Adunni Komolafe da Nonyem Onyechi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng