Bai dawo makaranta ba a wannan zangon: Dalibai da Malamai kan yaron El-Rufa'i

Bai dawo makaranta ba a wannan zangon: Dalibai da Malamai kan yaron El-Rufa'i

- Wasu malamai da dalibai a makarantan da 'dan El-Rufa'i yake sun ce sun daina ganinsa

- Yan bindiga sun kai hare-hare da niyyar garkuwa da daliban makaranta da dama a jihar Kaduna

Tun da aka koma karatu a wannan zangon, Abubakar El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, bai koma makaranta ba, binciken SaharaReporters ya nuna.

A 2019, gwamna El-Rufa'i ya kai yaronsa makarantar Kaduna Capital School bayan alkawarin da yayi.

An samu labarin cewa rashin zuwan yaron makaranta ba zai rasa alaka da matsalar tsaro da garkuwa da daliban makaranta da akeyi a jihar Kaduna da sauran jihohin Arewa ba.

A ranar Litinin, wasu dalibai da Malaman makarantar sun bayyanawa wakilin SaharaReporters cewa Abubakar El-Rufa'i bai dawo makaranta ba tun da aka fara sabon zango.

DUBA NAN: Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

Bai dawo makaranta ba a wannan zangon: Dalibai da Malamai kan yaron El-Rufa'i
Bai dawo makaranta ba a wannan zangon: Dalibai da Malamai kan yaron El-Rufa'i Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya ba da umarnin murkushe 'yan fashi, masu satar mutane

Daya daga cikin daliban yace: "Ya daina zuwa. Ba na ganinsa. Ban sani ko har yanzu dan makarantar nan bane."

"Ajinsa na gidan benen nan, sashen daliban firamare. Amma bai zo makaranta ba tun da muka dawo," wani dalibin ya kara.

"Ka san matsalar tsaro a makarantun gwamnati a jihar; da yiwuwan iyayensa sun cireshi don gudun abinda ka iya biyo baya idan aka sace yara," wani malami a makarantar ya fada.

"Kila iyayensa sun sa shi wata makarantar, kila kuma ya dawo, bayan makarantu sun samu tsaro. Gwamnan ya bayyana matsayansa kan yan bindiga - ba zai biya kudin fansa ba. Saboda haka da yiwuwan ya yanke shawaran kare 'dansa," Wani malamin ya kara.

A bangare guda, Mahaifin daya daga cikin daliban makarantar FCFM Afaka 39 da yan bindigan suka sace a jihar Kaduna, Ibrahim Shamaki, ya mutu.

Channels TV ta rahoto cewa Ibrahim, mahaifi ne ga Fatima Shamaki, daya daga cikin dalibai matan da suka bayyana a bidiyon da yan bindigan suka saki.

A cewar majiya daga iyalan mamacin, Ibrahim Shamaki ya mutu sakamakon bugun zuciya bayan rashin lafiyan da ya fada bayan samun labarin sace diyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel