Yaron Jonathan ya yabi Tinubu, ya fadi sirrin doke jigon APC a 2023, ya ce zai yi kyau da mulki
- Dr. Doyin Okupe ya ce sai Bayarabe irinsa ne zai iya buge Bola Tinubu a 2023
- Okupe ya ce kalubalen da ke jiran Tinubu a zaben 2023 za su fito ne daga APC
- Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce Jigon na APC zai dace da rike Najeriya
Tsohon mukarrabin Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, ya ce ‘yan siyasar Kudu maso yamma ne kadai za su iya samun nasara a kan Asiwaju Bola Tinubu.
Dr. Doyin Okupe ya ce idan har tsohon gwaman na Legas ya fito takarar shugaban kasa, babu wadanda za su iya doke shi illa ‘yan siyasar kasar Yarbawa.
Doyin Okupe wanda ya yi aiki da Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa ya na sha’awar neman takarar shugaban kasa a 2023.
KU KARANTA: Gwamnan Legas, Sanwo-Olu ya yabi Tinubu
Da ya ke wasu bayanai a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 28 ga watan Maris, 2021, Doyin Okupe ya tabbatar da cewa Bola Tinubu abin fargaba ne a zabe.
Duk da karfin fitaccen jigon na APC a kudancin Najeriya, Okupe ya ce zai iya samun galaba a kansa.
“Na yi imani na kere masa kadan; na fi shi sanin siyasar kasa da takarar shugaban kasa, wajen tara masu kwakwalwa, za mu zo daya, idan ban ma sha gabansa ba.”
“A bangarena, zan yi masa lahani saboda ni kadai ne ke Bayaraben da ke neman shugaban kasa a PDP.”
KU KARANTA: Okupe ya bada hakuri bayan ya ce Ibo ba za su samu mulki ba
“Bayan wannan, ina ganin cewa Tinubu abokin gaba ne mai ban tsoron gwabza wa a zaben 2003. Tinubu ya na cikin ‘yan siyasar da su ka fi kowa a zamanin nan.”
“Dabararsa da sanin aiki, abin a yaba ne, a takaice, Tinubu zai dace da Shugaban kasa.” Inji Okupe.
Dr. Okupe ya ce matsalar da Tinubu zai samu shi ne ba ya magana kan batun Yarbawa, sannan akwai ‘yan jam’iyyarsa da ya taimaka da ke neman ganin bayansa.
Ku na da labari cewa tun kafin a kai ko ina, an samu sabani a tsakanin manyan PDP game da yankin da za a ba takara a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.
Watakila PDP ta yi fatali da tsarin kama-kama da ake yi tsakanin Arewa da Kudu, musamman idan ta yi amfani da shawarar kwamitin Gwamna Bala Mohammed.
Asali: Legit.ng