Gwamnatin Buhari za ta taimakawa ‘Yan kasuwar da gobara ta yi masu asara a Katsina, Zamfara

Gwamnatin Buhari za ta taimakawa ‘Yan kasuwar da gobara ta yi masu asara a Katsina, Zamfara

- Sadiya Umar-Farouq ta fitar da jawabi bayan gobarar Katsina da Zamfara

- Ministar ta ba hukumar NEMA umarni ta agazawa ‘Yan kasuwar Katsina

- Wata mummunar gobara da ta ci shaguna ta jawo asarar dukiyar miliyoyi

An ba hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa na kasa umarni ta taimaka wa wadanda gobarar da aka yi a babbar kasuwar Katsina ta jawo masu asara.

Jaridar Katsina Post ta bayyana cewa Ministar bada tallafi, agajin gaggawa, da walwalar al’umma, Sadiya Umar-Farouq ta bada wannan umarni.

Hajiya Sadiya Umar-Farouq ta bukaci hukumar NEMA ta bada tallafi ga wadanda su ka rasa dukiyarsu a gobarar da aka yi a jihohin Katsina da Zamfara.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a barikin sojoji da ke Zaria

Sadiya Umar-Farouq ta bayyana wannan ne a wani jawabi da ta fitar ta hannun hadimarta, Nneka Anibeze, a ranar Talata, 23 ga watan Maris, 2021 a Abuja.

Nneka Anibeze ta ce Ministan ta na mai takaici da bakin cikin asarar da wannan gobarar ta jawo.

Ga abin da jawabin ya ke cewa: “Na samu labari mara dadi na gobarar da aka yi a babbar kasuwar Katsina da ta Tudun Wada, a garin Gusau, jihar Zamfara."

“A madadin ma’aikata, ina mika sakon Allah ya-kyauta ga mutane da gwamnatin jihohin Katsina da Zamfara, musamman ‘yan kasuwar ‘Central’ ta Katsina."

KU KARANTA: Da zarar an ga ka na cabawa a gari, EFCC da ICPC za su iya cafke ka

“Na bada umarni ga NEMA ta bada agaji, sannan ta cigaba da bibiyar abubuwan da su ke wakana.” Ministar ta ce gobarar ta zo a lokacin da ake fama da COVID-19.

Ministar ta ce binciken da ake yi ya nuna shaguna 60 sun kone, wanda hakan ya jawo asarar miliyoyi.

Wannan na zuwa ne bayan tawagar gwamnatin tarayya da Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya jagoranta, ta je ta yi wa mutanen Katsina Allah-kyauta.

Idan ba ku manta ba, mummunar gobara ta barke a babbar kasuwar jihar Katsina wanda ake kira 'Central Market' a safiyar ranar Litinin, 22 ga watan Maris, 2021.

Rahotanni sun bayyana cewa, shaguna da yawa sun kone kurmus, yayin da ake kokarin kashe wutar. Ba a taba ganin irin wannan gobara a tarihin Katsina ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel