'Yan Daba Sun Kaiwa Shugaban Karamar Hukuma Hari a Niger

'Yan Daba Sun Kaiwa Shugaban Karamar Hukuma Hari a Niger

- 'Yan daba sun kai wa shugaban karamar hukumar Shiroro a jihar Niger, Suleiman Chukwuba hari sun fasa gilashin motar da ya ke ciki

- Hakan ya faru ne a lokacin da shugaban ke kokarin shiga ofishinsa a ranar Litinin bayan dakatarwa da aka masa na watanni 3

- Rahotanni sun ce ana zargin mataimakinsa, Isiaka Bawa ne ya gayyato yan daban saboda ya hana shi shiga ofishinsa

'Yan daba masu yawa a ranar Litinin sun kai wa Shugaban karamar Shiroro na Jihar Niger, Suleiman Chukwuba hari a yayin da ya ke komawa ofishinsa bayan dakatar da shi na watanni uku.

A yayin da shugaban karamar hukumar ke shigowa ofishinsa a ranar Litinin, 'yan daban da ake zargin mataimakinsa Isiaka Bawa ya gayyato, sun kai masa hari da sanduna da duwatsu

'Yan Daba Sun Kaiwa Shugaban Karamar Hukumar Hari a Niger
'Yan Daba Sun Kaiwa Shugaban Karamar Hukumar Hari a Niger. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa

'Yan daban sun mamaye sakatariyar, suna ta harbi da duwatsu suna dukan magoya bayan shugaban karamar hukumar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Idan za a tuna, kwamitin shugabannin karamar hukumar ce ta dakatar da Chukwuba a ranar 29 ga watan Disamban 2020 kan zarginsa da bannatar da kudade.

Majalisar dokokin jihar bayan yin bincike a kan barun ta ce shugaban karamar hukumar ba shi da laifi kuma dakatarwar da kwamitin karamar hukumar Shiroro ta masa ya saba doka.

Kazalika, wata babban kotu itama ta soke dakatarwa da aka yi wa shugaban karamar hukumar yayin da ta dakatar da mataimakinsa.

Rahotanni sun nuna cewa mataimakinsa, tunda farko ya umurci dukkan ma'aikata su fice daga sakatariyar karamar hukumar domin yana son ya rufe ofishin amma ba su kula shi ba don haka ya tafi ya gayyato yan daba don ganin shugaban karamar hukumar bai dawo ofis ba.

KU KARANTA: Shugabannin Kiristoci a Legas Sun Ce Suna Son Musulmi Ya Zama Gwamna a 2023

An kai wa motar da ke dauke da shugaban karamar hukumar hari a lokacin da ta ke shigowa sakatariya.

Yan daban sun yi amfani da sanduna sun fasa gilashin motar da ya ke ciki a kokarinsa na dukan shugaban karamar hukumar.

Magoya bayan Chukwuba sun kare shi har sai da ya shiga ofishinsa.

An gayyoto yan banga domin su kwantar da tarzomar amma hakan bai hana yan daban jifa da sukan mutane a sakataryar ba.

A jawabinsa bayan ya shiga ofis lafiya, shugaban karamar hukumar ya ce ya yafe wa dukkan wadanda ke da hannu wurin dakatar da shi inda bukaci su hada hannu wuri guda don magance kallubalen da jam'iyyar ke fuskanta.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel