Kungiya ta koka, ta ce ana shiri ta bayan-gida a PDP domin a ba wani ‘Dan Arewa takara a 2023

Kungiya ta koka, ta ce ana shiri ta bayan-gida a PDP domin a ba wani ‘Dan Arewa takara a 2023

- Igbo Leadership Development Foundation ta ce akwai wani lauje cikin nadi a PDP

- Shugaban ILDF ya ce ana shirin hana Kudu neman takarar Shugaban kasa a 2023

- Kungiyar ILDF take cewa kwamitin Bala Mohammed na so a sake kai tikiti Arewa

Wata kungiyar mutanen Ibo mai suna Igbo Leadership Development Foundation (ILDF), ta soki aikin da kwamitin gwamna Bala Mohammed ya yi wa PDP.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, shi ne ya jagoranci kwamitin da ya duba abin da ya wakana da jam’iyyar PDP a babban zaben 2019 da ya wuce.

Shugabannin wannan kungiya; Dr. Godwin I. Udibe, Onyebuchi Obeta, da Law Mefor, sun kira taron ‘yan jarida, su ka yi tir da aikin da kwamitin nan ya yi.

KU KARANTA: Ka da PDP ta tsuke masu neman takarar Shugaban kasa a 2023 - Kwamiti

Mohammed da kwamitinsa sun bada shawarar a bude kofar neman tikitin takarar shugaban kasa a karkashin PDP a zaben 2023 ga duk wanda ya ke da sha’awa.

Dr. Godwin I. Udibe da sauran takwarorinsa su ka ce wannan shawara, yunkuri ne na kassara ‘yan siyasar Kudu, musamman mutanen yankin Kudu maso gabas.

ILDF ta ke cewa: “Mun damu matuka da shawarar da kwamitin Bala Mohammed wanda jam’iyyar PDP ta kafa domin duba abin da ya faru a zaben 2019, ta bada.”

“A takaice, kwamitin da ya duba zaben ya bada shawarar ayi watsi da batun karba-karba wajen neman tikitin shugaban kasa a 2023.” Inji Dr. Godwin I. Udibe.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da Matasa za su marawa baya a zaben 2023

Kungiya ta koka, ta ce ana shiri ta bayan-gida a PDP domin a ba wani ‘Dan Arewa takara a 2023
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed
Source: Facebook

“PDP ta shirya aiwatar da shawarar da aka bada a rahoton binciken da aka gabatar bayan ta karbi aikin kwamitin da kafa ya duba zaben shugaban kasa da aka yi.”

Shugabannin wannan kungiya su ka ce: “Mu na sane cewa akwai yunkurin da ake yi a boye ta cikin-gida wajen sake ba ‘dan Arewa tikitin takarar shugaban kasa.

“Shiyasa kwamitin Bala Mohammed ya ambaci yankin Arewa maso gabas karara, ya ce ya kamata ayi la’akari da su idan har tsarin kama-kama zai yi aiki.”

A jiya ne aka ji cewa Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya bugi kirji, ya ce jam'iyyar PDP ba ta isa ta karbe kujerar Shugaban kasa a zaben 2023 a hannunta ba.

Badaru ya ce tun da aka ba Najeriya ‘yancin kai, ba a taba dacen da ya fi zuwan Muhammadu Buhari ba, don haka yake ganin APC za ta lashe zabe na gaba da za ayi.

Source: Legit.ng News

Online view pixel