Ana kukan an hana Malamai kudinsu na shekaru 5, Gwamna ya rabawa kowane Mawaki N10m

Ana kukan an hana Malamai kudinsu na shekaru 5, Gwamna ya rabawa kowane Mawaki N10m

- Nyesom Wike ya ba Mawakan da su kayi wasa a Fatakwal makukuwar kyauta

- Kowane mawakin ya tashi da Naira miliyan 10 a bikin da aka yi a ranar Asabar

- Gwamnan Ribas ya yi rabon wannan kudi ne sa’ilin da Malaman jihar ke kuka

Mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kira wani biki wanda manyan mawaka da-dama su ka halarta a garin Fatakwal a karshen makon da ya wuce.

Gwamna Nyesom Wike ya shirya wannan biki ne a ranar Asabar, 27 ga watan Maris, 2021.

Shahararren mawakin Najeriya, Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy, da wasu fitattun taurari sun samu halartar wannan biki da gwamnan Ribas ya shirya.

KU KARANTA: Bawa: Da zarar an bukaci in yi abin da ya saba doka, zan bar aiki

A wajen wannan biki, gwamnan na jihar Ribas ya bayyana yadda gwamnatinsa da sauran mutanen yankin Neja-Delta su ke alfahari da mawakan da ake ji da su.

Kamar yadda wani bidiyo ya nuna, da yake jawabi, Wike, ya yi alkawarin zai ba duk wani mawakin da ya halarci wannan biki kyautar kudi Naira miliyan goma.

Jaridar Pulse ta kawo rahoto cewa Mista Wike ya kuma yi alkawarin zai ba Damini Ogulu watau Burna Boy kyautar fili a birnin Fatakwal domin ya gina wa kansa gida.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa tsofaffin hafsoshin tsaro su ka gaza - Wike

Ana kukan an hana Malamai kudin shekaru 5, Gwamna ya rabawa kowane Mawaki N10m
Wike da su Burna Boy Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Ga abin da Wike ya ce da yake jawabi: “Ba siyasa na zo yi a nan ba. Kun san idan siyasa ce, na iya buga ta. Babu wanda ya isa ya kalubalance mu a jihar nan.”

“Wadanda su ka zo, abin da ku ka yi da ma’aikatar al’adu da yawon bude idanu, ba matsala ta ba ce, amma duk wadanda su ka zo (nan) yau da mutanen Neja-Delta da ku ka zo nuna baiwar da ku ke da ita, ina alfahari da ku.”

Wike ya cigaba: “Kowanenku, kowane daga cikinku, zai tafi gida da Naira miliyan goma a aljihunsa.”

Gwamnan na kiran wannan kudi, mutane su ka kaure da shewa. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da malamai su ke kukan su na bin jihar kudin shekaru biyar.

Kwanaki kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bada sanarwar za ta koma biyan ma'aikatanta mafi karancin albashin N18,000 a maimakon N30,000 da aka fara biya.

Uzurin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje shi ne annobar Coronavirus ta yi mummunar illa ga tattalin arzikin Najeriya, wanda hakan ya taba jihar Kano sosai.

Source: Legit

Online view pixel