Majalisa ta kira taron gaggawa saboda jita-jitar tunbuke Gwamnan Borno, Bagagana Zulum

Majalisa ta kira taron gaggawa saboda jita-jitar tunbuke Gwamnan Borno, Bagagana Zulum

- Majalisar dokokin jihar Borno ta kira zama na gaggawa a ranar Juma’a da safe

- Hakan na zuwa ne a dalilin rade-radin da ake yi na shirin tsige Gwamnan Borno

- ‘Yan majalisar duk sun nesanta kansu daga yunkurin tunbuke Babagana Zulum

A ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, 2021, majalisar dokokin jihar Borno, BOSHA, ta musanya zargin da ake yi na shirin tunbuke gwamna Babagana Zulum.

Jita-jita suna yawo a kafafen yada labarai da sadarwa na zamani cewa ‘yan majalisar dokoki 23 cikin 29 sun shirya tsige Babagana Umara Zulum daga kan mulki.

Shugaban majalisar dokokin na Borno, Rt. Hon Abdulkarim Lawan, ya ce ko da ma’aikatan majalisa su na yajin-aiki a fadin Najeriya, dole su ka yi zama a yau.

KU KARANTA: Rashin tsaro: ‘Yan Majalisa sun kama hanyar canza aikin ‘Dan Sanda

Hon Abdulkarim Lawan ya ce sun taru a zauren majalisar ne su ka yi zaman gagagwa domin muhimmancin su yi wa jama’a bayani gaskiyar halin da ake ciki.

Jaridar Vanguard ta ce a zaman gaggawan da aka yi, duka ‘yan majalisar jihar Borno sun tabbatar da cewa su na tare da Mai girma Farfesa Babagana Umara Zulum.

Honarabul Dige Mohammed mai wakiltar mazabar Kala Balge shi ne ya bukaci ayi wannan zabe a matsayin batutuwan gaggawa masu muhimmanci ga al’umma.

‘Dan majalisa mai wakiltar Abadam, Ahaji Jamuna Bang ya goyi bayan kiran Dige Mohammed.

Majalisa ta kira taron gaggawa saboda jita-jitar tunbuke Gwamnan Borno, Bagagana Zulum
Mai girma Gwamnan Borno, Bagagana Zulum Hoto: @GovBorno
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mai neman ganin bayan Gwamnatin Buhari ya jira 2023 - Garba Shehu

Da aka yi zabe, duka ‘yan majalisa sun kada kuri’ar ba gwamna Babagana Zulum goyon-baya, su ka ce babu hannunsu a rade-radin da ake yi na tsige shi daga mulki.

‘Yan majalisar su ka ce su na tare da Babagana Umara Zulum wajen samar da zaman lafiya a Borno, su ka yi kira ga jami’an tsaro su kama masu yada labaran bogi.

A makon nan ne aka samu labarin cewa gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jaddada kiran a maida mulkin kasar nan zuwa yankin kudu a 2023.

Gwamnan na APC ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yayi jawabi wajen kaddamar da littafin da tsohon shugaban NIMASA, Dakuku Peterside ya wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng