Amaechi ya ce za a kammala jami’ar sufuri na Daura a 2021
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ana sa ran za a kammala aikin jami’ar sufuri ta tarayya a Daura a watan Satumban 2021
- Ministan sufuri ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ganin aikin a Daura
- Amaechi ya ce masu aikin ginin sun bashi tabbacin cewa za sub a aikin cikakken kulawa
Ministan sufuri, Rotimi Amarchi ya bayyana cewa ana sanya ran za a kammala jami’ar sufuri na tarayya a Daura a watan Satumban 2021.
Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 29 ga watan Agusta, lokacin da ya kai ziuyarar ganin ginin a Daura domin tabbatar da fara aiki kan kwangilar, NAN ta ruwaito.
Ya ce ma’aikatan na kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation(CCECC) da ke aikin ginin sun samu amincewar gwamnatin jihar kuma za su fara aiki a karshen watan Satumban 2020.
"Wannan ba aikin jirgin ƙasa ba ne. Kyauta ce daga gare su (CCECC)," in ji Amaechi.
KU KARANTA KUMA: Jahilai ne masu ruwa da tsaki a kasuwancin magunguna a Kano - PCN
Ministan ya bayyana cewa ba lallai ne masu aikin ginin su jajirce kamar yadda za su nuna idan aka zo kan aikin kwangila na ainahi domin wannan aikin kyauta ne.
Sai dai ya ce masu aikin sun bashi tabbacin cewa za su ba aikin irin kulawar da suke ba aikin jirgin kasa.
A wani labari na daban, mun ji cewa tuni aka kammala dukkanin wasu gyare gyare a babbar tashar jiragen sama ta Akanu Ibiam, mizanin da za a iya bude tashar a yanzu.
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, wanda ya isa tashar jiragen a ranar Asabar domin duba matakin da aikin yake, ya ce komai ya yi dai dai yanzu, za a iya fara jigilar mutane.
A watan Agusta, 2019 ne aka rufe tashar jiragen domin baiwa gwamnati damar gudanar da gyare gyare, musamman tituna da kuma wasu gine gine da ke cikin tashar.
Ministan ya sanar da cewa a ranar 30 ga watan Agusta, 2020 ne za a bude tashar jiragen domin fara jigilar mutane da kaya.
A yayin ziyarar gani da idon tare da wasu kososhin gwamnatin jihar Enugu, Sirika ya ce ya gamsu da matakin aiki, yanzu za a iya bude tashar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng