Buhari bai fahimci hoton da Ganduje ya nuna masa ba, Kwankwaso

Buhari bai fahimci hoton da Ganduje ya nuna masa ba, Kwankwaso

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, ya zargi shugaba Buhari da rashin gane hoton gadar sama da Ganduje ya kai masa

- Tsohon gwamnan jihar Kano yace alhakin gwamnatin tarayya ne na yin gadar da zata hada garin Kano da na Wudil

- Sanata Kwankwaso ya caccaki Gwamna Ganduje ta yadda bai je wa Buhari da bukatar gadar ba amma zai karbo bashi don yin ta

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin fahimtar hoton da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gabatar masa a fadar shugaban kasan dake Abuja.

Tun a farkon makon nan, Buhari ya karba bakuncin Ganduje wanda ya nuna masa hoton gadar Muhammadu Buhari da za a yi a jihar Kano.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso yayi mamakin dalilin da zai sa a karba bashin N20 biliyan a kan aikin nan, wanda yace aikin gwamnatin tarayya ne.

KU KARANTA: Buhari na daga cikin alheran da suka taba faruwa da Najeriya, Badaru

Buhari bai fahimci hoton da Ganduje ya nuna masa ba, Kwankwaso
Buhari bai fahimci hoton da Ganduje ya nuna masa ba, Kwankwaso. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Ya zargi Ganduje da baiwa abubuwan da basu dace ba fifiko inda yace ilimi da walwalar jama'a ce ya dace ta zama a sahun gaba.

"A maimakon Ganduje yaje ya gana da Buhari ya sanar dashi cewa yayi gadar, saboda alhakin gwamnatin tarayya ne yin gadar sama da zata hada garin Kano da Wudil, gwamnan ya tashi ya kai masa hoton da ba a zana da kyau ba, wanda shugaba Buhari bai gane ba."

A wani labari na daban, shugaban kasa M,uhammadu Buhari yace ta'addanci, mayar da jama'a 'yan gudun hijira da sauyin yanayi manyan kalubale ne ga jama'a da alakar dake tsakaninsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce akwai matukar amfani kasashen duniya su yi aiki tare domin samo hanyoyin da ya dace wurin shawo kan wadannan kalubalen.

Ya sanar da hakan ne yayin jawabi a wani shagalin karbar wasikar jinjina a gidan gwamnati dake Abuja, inda yace wannan kalubalen manyan matsaloli ne ga al'umma.

Buhari ya karba wasikar ne daga babban kwamishinan The Gambia, Mohamadou Musa Njie; jakadan kasar Korea ta kudu, Kim Young-Chae; jakadan Slovak, Tomas Felix; Babban kwamishinan Australia, John Gerard Donnelly; babban kwamishinan Bangladesh, Masudur Rahman da jakadan Guinea Bissau, Jaao Ribeiro Butiam Co.

Asali: Legit.ng

Online view pixel