Mummunar annobar ambaliya ta na jiran al’umma a shekarar 2021 inji Hukuma
- Hukumar HIHSA tace za a gamu da annoba a cikin shekarar nan ta 2021
- Shugaban HIHSA ya ce gwamnati da mutane su fara shiryawa ambaliyar
- Clement Nze ya bada shawarar yadda za a takaita barnar wannan annoba
A ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021, hukumar NIHSA da ke lura da sha’anin ruwa na kasa, ta bayyana cewa za a gamu da ambaliya a shekarar nan.
NIHSA ta yi kira ga gwamnatocin Najeriya su tashi-tsaye, su shirya wa ambaliyar da ke tafe. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.
Darekta Janar na hukumar NIHSA, Clement Nze, ya bada wannan sanarwa maras dadi a lokacin da ya kira taron manema labarai a birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 54, ta lalata gidaje 30,356 a Kano
Clement Nze yake cewa ambaliyar da za ayi za ta addabi jihohin Najeriya ne saboda a nan ne duk ruwan da ya taso daga sauran kasashen Afrika tara ya tsaya.
“Har yanzu akwai lokaci da jihohi da kananan hukumomi da sauran daidaikun mutane za su iya daukar matakan da za a kare wannan musibar annoba a bana.”
Ruwan da ya taso daga Benin, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Cote D’Ivoire, Guinea, Mall, da Niijar duk ya tike ne a kogin Najeriya, wanda hakan ke jawo ambaliya.
NIHSA ta bada shawarar a rika gina hanyoyin ruwa, a gyara kwatoci da bola. Haka zalika an bukaci mutane su cire ciyayi da tarkance da ke hanyoyin ruwa.
KU KARANTA: Buhari ya aikawa Kaduna, Kano, Kebbi wasu jihohi tallafi bayan ambaliya
Mista Clement Nze, ya ke cewa ambaliya ta zama ruwan dare a Najeriya tun shekarar 2012 lokacin da aka gamu da babbar musibar da ba a taba ganin irin ta ba
A cewar Nze, an yi asarar rayukan daruruwan mutane da kayan bilyoyi, sannan mutane da-dama sun koma ba su da matsuguni a sakamakon wannan ambaliya.
A bara idan za ku tuna, hukumar bada agaji na gaggawa na kasa watau NEMA ta ce za ayi ambaliyar ruwan sama a kananan hukumomi 102 da ke jihohi 28.
A jawabin da Daraktan ya gabatar, ya ce sun yi hasashen wannan ne sakamakon rahoton da ma'aikatar lura da karkokin ruwa a Najeriya, NIHSA ta fitar.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng