Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Karɓi Baƙuncin Shugaba Idriss Deby a Fadarsa ta Aso Rock

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Karɓi Baƙuncin Shugaba Idriss Deby a Fadarsa ta Aso Rock

- Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwararsa Idriss Deby na kasar Chadi a fadarsa da ke Abuja

- Shugaba Idriss Deby ya isa fadar Aso Rock a birnin tarayya Abuja misalin karfe 12.15 na rana

- Yayin tarbar bakonsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da wasu yan fadarsa ga Idris Deby

Shugaba Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawa tare da shugaban kasar Jamhuriyar Chadi, Idriss Deby a fadar shugaban Najeriya da ke birnin tarayya Abuja, The Nation ta ruwaito.

Shugaba Deby ya isa gidan gwamnatin misalin karfe 12.15 na rana kuma mai masaukin baki, Shugaba Muhammadu Buhari ya tarbe shi inda ya gabatar da wasu yan fadarsa gare shi.

DUBA WANNAN: Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Karbi Bakuncin Shugaba Idris Deby a Fadarsa ta Aso Rock
Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Karbi Bakuncin Shugaba Idris Deby a Fadarsa ta Aso Rock. hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Wadanda suka tare da Shugaba Buhari yayin da ya ke tarbar bakonsa sun hada da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, Direktan Hukumar Leken Asiri na Kasa, NIA, Ahmed Rufai.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa

Saura sun hada da Ministan Birnin Tarayya Abuja, Mohammed Bello, Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguna (mai murabus) da kuma jakadan Nigeria ga kasar Chadi.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel