Gwamnan Jigawa ya bugi kirji, ya ce PDP ba ta isa ta karbe kujerar Shugaban kasa a 2023 ba

Gwamnan Jigawa ya bugi kirji, ya ce PDP ba ta isa ta karbe kujerar Shugaban kasa a 2023 ba

- Gwamnan Jigawa ya ce PDP, ba ta isa ta raba APC da mulkin kasar nan a 2023 ba

- Mohammed Badaru Abubakar ya ce gaskiya da amanar APC ne za su ba ta nasara

- Gwamnan ya ce tun 1960, ba ayi dacen Shugaban kasa irin Muhammadu Buhari ba

Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsare-tsare da dabaru na APC, Mohammed Badaru Abubakar, ya ce PDP ba za ta iya cin zabe ba.

Jaridar The Nation ta rahoto Mohammed Badaru Abubakar ya na cewa mutane da-dama za su bar jam’iyyar hamayya ta PDP, su tsallako su dawo APC.

Gwamnan ya bayyanaa wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a ranar Alhamis a gidan talabijin.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya dage a kan sai mulki ya bar Arewa a 2023

“Ban ga PDP ta na yunkurin karbar mulki ba, ko a makon jiya, mun samu tsohon gwamnan Ondo, wanda ya yi wa Atiku darektan kamfe, ya shigo APC.”

Bayan sauyin-shekarsu Gbenga Daniel, gwamnan ya ce: “Mutane su na fice wa daga PDP su shiga APC. Gaskiya da amanarmu za ta sa mu zarce a 2023.”

Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi gum da batun cewa mulki zai koma Kudu ne a 2023.

Gwamnan ya ki fadan ra’ayinsa; Ya ce: “Ina cikin kwamitin dabaru da za su duba wannan batu, da a ce a watan da ya wuce aka tambaye ni, da na bada amsa.”

KU KARANTA: An samu 'Dan shekara 35 da ke harin kujerar Shugaban kasa

Gwamnan Jigawa ya bugi kirji, ya ce PDP ba ta isa ta karbe kujerar Shugaban kasa a 2023 ba
Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar Hoto: Fadar Shugaban kasa

Badaru Abubakar ya ce tun da kasar nan ta samu ‘yanci, ba a taba sa’ar shugaban kasa irin Muhammadu Buhari ba, ya ce shi ne babban dacen da aka yi.

A hirar da aka yi da shi, gwamnan ya fadi irin ayyukan alherin da gwamnatin Buhari ta yi, ya ce akwai lokacin da shi kanshi ya ji kamar ya ajiye kujerar gwamna.

A 2020 ne aka ji gwamnan na Jigawa, Badaru Abubakar ya na cewa rikicin cikin gidan da ke damun APC a jiharsa zai iya yin sanadiyar shan kashinta a 2023.

Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana cewa APC na iya rasa jihar Jigawa a zaben 2023 idan har ba a dauki matakin gaggawa game da rikicin da ya kunno kai ba.

Source: Legit

Online view pixel