Daya daga cikin tsofaffin Ministan Shagari da su ka rage, Olowoporoku, ya bar Duniya

Daya daga cikin tsofaffin Ministan Shagari da su ka rage, Olowoporoku, ya bar Duniya

- A ranar Alhamis, 25 ga watan Maris, Sanata Bode Olowoporoku ya rasu ya na 75

- Dr. Bode Olowoporoku ya taba rike kujerar Sanata da Ministan Tarayya a Najeriya

- Marigayin ya na cikin wadanda su ka dage har Janar Sani Abacha ya ba Ekiti jiha

A ranar Juma’a, 26 ga watan Maris, 2021, mu ka samu labari cewa Bode Olowoporoku wanda ya yi Ministan tarayya a jamhuriyya ta biyu ya rasu.

Sanata Bode Olowoporoku ya rasu ne a ranar Alhamis a Legas bayan ya yi fama da gajerar rashin lafiya. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto.

Sanarwar mutuwar dattijon ta fito ne ta bakin daya daga cikin ‘ya ‘yansa, Ayodeji Olowoporoku.

KU KARANTA: Bashi ya sa an yanke wutan gidan tsohon Shugaban kasa Shagari

“Mu na bakin cikin sanar da mutuwar mai gidanmu, mahaifinmu, kakanmu, kawunmu, abokinmu, Dr. Olabode Olowoporoku wanda ya mutu a gidansa.”

Mista Ayodeji Olowoporoku.yake cewa: “Ya cika ne salin-alin a gidansa a ranar 24 ga watan Maris, 2021, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.”

Marigayin ya yi karatu a jami’ar Ife, ya yi digiransa na farko a fannin tattalin arziki, daga nan ya tafi Manchester a Ingila ya yi digirin M.Sc. da Ph.D a 1975.

Dr. Olowoporoku ya na cikin wadanda su ka yi ruwa da tsaki wajen ba Ekiti jiha mai zaman kanta a 1996.

KU KARANTA: EFCC ta kira wanda ya bada shaida a shari'ar zargin sata da Suswam

Daya daga cikin tsofaffin Ministan Shagari da su ka rage, Olowoporoku, ya bar Duniya
Sanata Bode Olowoporoku Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Bode Olowoporoku ya rike kujerar Ministan kimiyya da fasaha a gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, marigayi Shehu Shagari a 1983 lokacin ya na 38.

Olowoporoku mutumin garin Ilawe Ekiti ne a jihar Ekiti. Kamar yadda mu ka samu rahoto an haifi wannan Bawan Allah ne a Satumban shekarar 1945.

Tsakanin 203 da 2007, marigayin ya wakilci yankin kudancin jihar Ekiti a majalisar dattawan Najeriya.

A yau kun ji akwai yiwuwar rigima ta na neman barkewa a PDP game da zaben 2023 tun a yanzu saboda shawarar da kwamitin Bala Mohammed su ka bada.

Ana zargin kwamitin Gwamna Mohammed da yunkurin murkushe mutanen Kudu a Jam’iyyar PDP bayan ya bada shawarar a bar kofar neman takara a bude.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng