Gwamnatin Sokoto ta Rufe Kwalleji Saboda Ɓarkewar Annobar Cholera

Gwamnatin Sokoto ta Rufe Kwalleji Saboda Ɓarkewar Annobar Cholera

- Gwamnatin Jihar Sokoto ta rufe kwallejin gwamnati ta mata da ke Mabera

- An rufe makarantar ne sakamakon bullar annobar Cholera da ta kashe dalibai biyu

- Dr Kulu Haruna, kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar ta ce an yi wa makarantar feshi nan gaba za a bude

Gwamnatin jihar Sokoto ta rufe kwallejin gwamnati na mata da ke Mabera bayan bullar cutar Cholera wacce a yanzu ta halaka mutane biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar, Dr Kulu Haruna ta ce matakin ya zama dole ne domin samun damar dakile matsalar.

DUBA WANNAN: A Karo na Biyu, Masu Garkuwa Sun Sace Jigon APC a Lokacin Da Ya Tafi Duba Gonarsa

Gwamnatin Sokoto ta Rufe Kwalleji Saboda Barkewar Annobar Cholera
Gwamnatin Sokoto ta Rufe Kwalleji Saboda Barkewar Annobar Cholera. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar ta, cutar ta shafi dalibai 70 amma 20 cikinsu ne suka cibiyar killacewa a halin yanzu.

Sauran, ta ce, tawagar ma'aikatan lafiya da aka tura makarantan sun musu magani an kuma sallame su.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa daliban biyu da suka rasu an turo su makarantar ne bayan rufe makarantu a wuraren da ake fargabar harin yan bindiga.

"Daliban sun zo ne daga makarantun kwana da ke kananan hukumomin Rabah da Bodinga, " in ji ta.

Haruna, ta ce ba gaskiya bane cewa daga rijiyar burtsatse cutar ta samo asali.

KU KARANTA: Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

A cewarta, cutar kawai kaddara ce kamar yadda ake samu a wasu wasu sassar jihar kamar Cibiyar Koyar da Karatun Kurani da Sauran Darrusa na Sultan Muhammadu Maccido da cutar ta kashe dalibi daya.

Ta ce an yi wa makarantar feshin magani sannan za a bude a nan gaba idan abubuwa sun daidaita.

Kimanin kwanaki uku da suka gabata cutar ta bulla, hakan ya tilastawa makarantar sauya daya daga cikin dakin kwanan dalibai zuwa cibiyar killace marasa lafiya.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel