Majalisar Dattawa ta na yunkurin ragewa Shugaban ‘Yan Sanda karfin iko a sabuwar doka

Majalisar Dattawa ta na yunkurin ragewa Shugaban ‘Yan Sanda karfin iko a sabuwar doka

- An gabatar da kudirin sauya dokar aikin Yan Sanda a Majalisar Dattawan Najeriya

- Sanata Surajudeen Ajibola Basiru ne ya kawo wannan kudiri domin inganta tsaro

- Sanatoci za su tattauna a kan ‘The Nigeria Police Act 2020 (Amendment) Bill, 2021

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majalisar dattawan kasar nan ta shigo da wani kudiri da zai yi wa dokar Police Act na shekarar 2020 garambawul.

Wannan sabon kudiri da aka yi wa take da ‘The Nigeria Police Act 2020 (Amendment) Bill, 2021’.

Rahoton ya ce wanda ya gabatar da kudirin a majalisar dattawan shi ne Sanatan jam’iyyar APC mai wakiltar yankin Osun, Surajudeen Ajibola Basiru

KU KARANTA: Sabon kwamishinan Taraba bai da wurin aiki, ya fara aiki a kasan bishiya

Burin kudirin shi ne a gyara aikin ‘dan sanda ta yadda za a cire abubuwan da ke kawo matsala wajen aikin tsaro, sannan za a rage wa IGP karfi a doka.

Hakan na zuwa ne watanni bayan shugaba Muhammadu Buhari ya sa hanu a Nigeria Police Bill 2020 wanda ya maye gurbin dokar da ta ke aiki a kasa.

Wani abin lura shi ne wannan kudiri na Surajudeen Basiru ya gabatar, zai magance matsalar rashin kudi da ake yawan fama da shi wajen ‘yan sanda.

Alhakin kasafin kudin zai koma ga manyan ofisoshin ‘yan sanda da za a bude idan har wannan kudiri ya samu karbu wa a majalisa da fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Kullu-yaumin sai an yi amfani da mutanen da aka yi garkuwa da su

Majalisar Dattawa ta na yunkurin ragewa Shugaban ‘Yan Sanda karfin iko a sabuwar doka
Shugaban ‘Yan Sanda na kasa, IGP, MA Adamu
Asali: UGC

Wannan kudiri ya bada damar kafa wata majalisar tsaro ta shiyyoyi, da masu ba gwamna shawara a kan yadda za a magance matsalar tsaro a kowace jiha.

Idan kudurin ya yi dace, masana su na ganin cewa an kama hanyar samar da ‘yan sanda na cikin gida.

Ga yadda za a raba shiyyoyin, inda za a zabi AIG (a karkashin IGP) ya rika kula da kowace shiyya.

Zone 1: Kano/Jigawa/Katsina; Zone 2: Lagos/Ogun; Zone 3: Adamawa/Taraba/Gombe;

Zone 4: Benue/Plateau/Nasarawa; Zone 5: Edo/Delta/Bayelsa; Zone 6: Rivers/Akwa-Ibom/Cross River;

Zone 7: Kaduna/Niger/FCT; Zone 8: Ekiti/Kwara/Kogi; Zone 9: Imo/Abia; Zone 10: Sokoto/Zamfara/Kebbi;

Zone 11: Oyo/Osun/Ondo; Zone 12: Bauchi/Yobe/Borno da Zone 13: Anambra/Enugu/Ebonyi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel