Gwamnan Delta ya ba Shugaba Buhari zabi 2 game da dukiyar satar Ibori da ya lakume

Gwamnan Delta ya ba Shugaba Buhari zabi 2 game da dukiyar satar Ibori da ya lakume

- Gwamna Ifeanyi Okowa ya tuntubi Gwamnatin tarayya kan kudin satar Ibori

- Delta ta bukaci Muhammadu Buhari ya dawo mata da kudin da su ka mallaka

- Okowa ya bada zabi ayi masu ayyuka ko a maidowa mutanen Delta kudin nasu

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce ya rubuta takardar korafi zuwa ga Muhammadu Buhari a kan batun kudin da James Ibori ya sace.

Ifeanyi Okowa ya tabbatar da wannan ne a lokacin da ya bayyana a cikin shirin siyasa na Politics Today a gidan talabijin na Channels TV a ranar Laraba.

A kwanakin baya gwamnatin tarayya ta yi nasarar fam miliyan £4.2 da tsohon gwamna James Ibori da mukarrabansa su ka sace daga asusun jihar Delta.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gagara shawo kan kasar nan - Dattawan Arewa

Da yake magana a game da batun wadannan kudi da Najeriya ta karbo, gwamnan na Delta ya ce:

“A bangarenmu, mun zauna da babban lauyan gwamnatin tarayya, Kwamishinan shari’a na ya hadu da shi. Mu na aiki, kuma za mu fahimci juna.”

“Mun rubuta takardar korafi zuwa ga shugaban kasa. Na mu shi ne mu yi wa gwamnatin tarayya bayani cewa ya kamata a ba jihar Delta wannan kudi.”

“Idan ba za a dawo wa Delta da kudin kai-tsaye ba, dole ayi amfani da shi, ayi ayyuka. Mun gabatar da shawarwari biyu; a ba mu kudin, ko ayi aiki.”

Gwamnan Delta ya ba Shugaba Buhari zabi 2 game da dukiyar satar Ibori da ya lakume
Gwamnan Delta Hoto: legit.ng

KU KARANTA: 2023: Alkawarin da aka yi da Buhari, Tinubu a kan takarar Shugaban kasa

“Amma a wannan wasika – saboda mun ga yarjejeniyar da aka shiga da gwamnatin Birtaniya, mun ga bukatar mu tunkari lamarin da hikima.” Inji Okowa.

“Shiyasa mu ka kawo maganar ayi mana ayyuka, idan ba zai yiwu a ba mu kudin ba.”

Kwanaki kun ji cewa kasar Burtaniya za ta dawowa Najeriya zuzurutun kudi £4.2m da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya sace a lokacin ya na ofis.

Hakan na kunshe ne a sanarwar da jakadar Birtaniya a kasar nan, Catriona Laing ta fitar. Wannan mataki na mallaka wa Najeriya kudin bai yi wa wasu dadi ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng