'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Lauya a Gaban Kotu Kan 'Satar Naira Miliyan 5'

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Lauya a Gaban Kotu Kan 'Satar Naira Miliyan 5'

- Yan sanda sun yi karar wani lauya a gaban kuliya kan zargin satar Naira miliyan 5

- Ana zargin lauyan da karkatar da wani kaso cikin kudin filin da wanda ya ke wakilta ya mallaka

- Wanda ake zargin ya roki kotu ta yi masa afuwa bayan haka kotu ta bada belinsa kan kudi N200,000

Rundunar yan sanda na jihar Ebonyi, a ranar Laraba ta gurfanar da wani lauya mai shekaru 52 a gaban kotu kan zargin satar Naira miliyan 5 mallakar wani Igwe Nwokpata a jihar.

Wanda aka yi karar, Barrista Onu Onwe, an gano cewa lauyan wanda ya yi karar ne kuma sun kasance tare tsawon shekaru 13, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Lauya Kan 'Satar N5m' a Ebonyi
'Yan Sanda Sun Gurfanar Da Lauya Kan 'Satar N5m' a Ebonyi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

An ce ya sayar da filin wanda ya yi kararsa a kan kudi Naira miliyan 29 amma Naira miliyan 24 kawai ya bashi.

Rikici ya fara ne a lokacin da lauyan ya bukaci wanda ya yi karar (Igwe Nwokpata) ya sa hannu kan takardar bawa lauya iko.

A lokacin da lauyan ya gane wanda ya yi karar ba zai sa hannu ba kawai sai shi da kansa ya saka hannun na bogi.

An ce ya aikata laifin ne a Nna Street, Abakaliki, karamar hukumar Abakaliki na jihar a ranar 25 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari A Kaduna, Sun Kashe Huɗu Sun Raunta Wasu

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Mathias Eze ya shaidawa kotu cewa laifin ya ci karo da sashi na 516A (a); 309 (9) da 467 (2)(d) na dokar masu laifi Cap. 33 Vol. 1 na dokokin jihar Ebonyi.

Wanda aka yi karar, ta bakin mai kare shi, shugaban kungiyar lauyoyi na Nigeria, NBA, reshen jihar Ebonyi, ya nemi sassauci.

Alkalin kotun, Mrs Nnenna Onuoha ta bada belin wanda aka yi karar kan kudi N200,000 tare ga wadanda zai tsaya masa.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel