Gawa ya farka yayin da ake bikin jana'iza: Mai aikin shirya gawa ya magantu

Gawa ya farka yayin da ake bikin jana'iza: Mai aikin shirya gawa ya magantu

- Wani mai aikin gyara kula da shirya gawa, Samuel Okyere ya bada labarin abubuwan mamaki da ya ke karo da su

- Okyere yayin hira da aka yi da shi ya ce sau da yawa yana shirya gawa, gawar na farkawa har su yi magana

- Ya bada labarin wani gawar da ya farka yayin da ya ke shirya shi, amma ya fada masa cewa shi dan sako ne don haka kada ya halaka shi

Samuel Okyere, wani mai aikin kula da gawa da shirya jana'iza ya magantu kan irin abubuwan mamaki da al'ajabi da ya gamu da su yayin aikinsa a hirar da aka yi da shi a Crime Check Television, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, a lokuta da dama ya kan shiga mawuyacin hali har ya rika fargabar zai mutu idan ya yi karo da gawar da ta tashi a lokacin da ya ke shirya ta domin jana'iza.

Gawa ya farka yayin da ake bikin jana'iza: Mai aikin shirya gawa ya magantu
Gawa ya farka yayin da ake bikin jana'iza: Mai aikin shirya gawa ya magantu. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Sumame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Da ya ke bada labarin arangamar da ya yi da wata gawar da ta farka, ya yi bayanin cewa sai da ya yi magana da gawar ya roki ta tausaya masa ta bar shi da ransa.

Ya ce yana shirya gawar sai ya fita ya dako wani abu ya dawo, sai ya ga cewa gawar na kyafa ido, "na ji tsoro amma na daure na yi ta maza."

Mai gabatar da shirin ya yi mamakin jin labarin inda ya fadawa Samuel akwai yiwuwar kankara ce ta narke daga cikin gawar shi yasa ya ke ganin kamar kyafta ido ta ke yi. Amma Samuel ya tubure ya ce ba sau daya ya yi karo da irin wannan ba kuma ya san banbancin narkewar kankara da kyafta ido.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

"Abinda za ka yi idan haka ya faru shine ka yi magana da gawar cewa idan yana da matsala da wani toh su sasanta kansu bayan jana'izan amma kai babu ruwanka."

"Don haka, na ce ya tafi ya sasanta da iyalansa ko wani da ya ke da matsala da shi kafin rasuwarsa. Na fayyace masa cewa ni dan sako ne da aka aiko ni in gyara gawarsa kafin jana'iza."

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel