'Dan sanda ya bindige abokin aikinsa har lahira yayin kokarin kama masu laifi

'Dan sanda ya bindige abokin aikinsa har lahira yayin kokarin kama masu laifi

- Jami'in dan sanda ya bindige abokin aikinsa bisa kuskure a garin Aba da ke jihar Abia

- Hakan ya faru ne a lokacin da yan sandan ke kokarin kama wasu da ake zargi da laifi

- Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da hakan amma bai yi cikakken bayani ba

Jami'in dan sanda a garin Aba, Jihar Abia, a jiya ya kashe wani abokin aikinsa yayin kokarin kama wani da ake zargi da aikata laifi.

Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Bata Junction, yayin da dan sandan ke kokarin harbin wanda ake zargin amma ya yi kuskure ya bindige abokin aikinsa.

'Dan sanda ya bindige abokin aikinsa har lahira yayin kokarin kama mai laifi
'Dan sanda ya bindige abokin aikinsa har lahira yayin kokarin kama mai laifi. Hoto: Vangaurdngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: 'Yan Hisbah Sun Kai Sumame Gidan Ɗaliban Jami'a, Sun Kama Mace da Namiji a Ɗaki Ɗaya

Wani da abin ya faru a idonsa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan sandan sun yi kokarin tsare wata mota kirar Jeep mai bakin gilashi suka kuma kokarin tilastawa wadanda ke cikin motar su fito su shigar motarsu ta sintiri.

Wani dan sandan daban da ke cikin motar Jeep din ya yi kokarin rokon abokan aikinsa su kyalle su amma ba su amince ba.

Da mutanen da ke cikin Jeep din suka ki shiga motar yan sandan shine daya daga cikin yan sandan ya fito da bindiga ya harbi abokin aikinsa cikin kuskure a maimakon harbin wanda suke son kama wa.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

A cewar shaidun ganin ido, "Da dan sandan ya harbi abokin aikinsa, nan take suka kyalle wanda suke zargin suka koma kokarin taimakon abokin aikinsu."

Dan sandan da aka harba ya rasu a hanyarsu na zuwa asibiti amma ba a iya tabbatar da hakan ba a lokacin hada wannan rahoton.

Kakakin yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce ba a masa bayani a hukumance ba don haka ba zai yi tsokaci kan lamarin ba a yanzu.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel