Da duminsa: Tinubu ya ziyarci jihar Katsina, ya bada gudunmuwan N50m

Da duminsa: Tinubu ya ziyarci jihar Katsina, ya bada gudunmuwan N50m

- Duk da cece-kuce kan alakarsa da Buhari, Tinubu ya kai ziyara jihar Katsina

- Ya samu kyayyawar tarba daga gwamnan jihar da mukarrabansa

- Tinubu ya kai ziyara ranar Laraba don jajantawa mutanen da gobara ta shafa

Babban jagora a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada gudunmuwan milyan 50 ga wadanda sukayi asarar dukiya a gobarar babbar kasuwar jihar Katsina.

Channles TV ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da hakan ne ranar Laraba yayinda ya kai ziyarar jaje ga gwamnatin jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar suka tarbe shi.

Kasuwar jihar Katsina ta ci bal-bal ne ranar Litinin inda akayi asarar dukiya na miliyoyin naira.

Yayin jajanta musu, Tinubu ya ce jama'a su cigaba da kasuwancinsu duk da asarar da akayi.

Ya bayyanawa manema labarai cewa ya kai wannan ziyara ne domin jajantawa wadanda wannan abu ya shafa, gwamnan, da kuma al'ummar jihar Katsina gaba daya.

Tinubu ya jaddada cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin yan Najeriya.

Da duminsa: Tinubu ya ziyarci Sarkin Katsina, ya bada gudunmuwan N50m
Da duminsa: Tinubu ya ziyarci Sarkin Katsina, ya bada gudunmuwan N50m
Asali: Original

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel