Ambaliya: Buhari ya aika da tallafi Kaduna, Kano, Kebbi da wasu jihohi 9

Ambaliya: Buhari ya aika da tallafi Kaduna, Kano, Kebbi da wasu jihohi 9

- Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti ta musamman da za ta raba kayan tallafi ga jihohi 12 da ambaliyar ruwa ya shafa

- Jihohin sun hada sune Kebbi, Niger, Kwara, Kogi, Edo, Anambra, Delta, Kano, Jigawa, Rivers, Bayelsa da Adamawa

- Buharin ya kuma bayyana alhininsa ga wadanda ambaliyar ta shafa, wanda wasu suka rasa iyalansu, gidajensu da dukiyoyi

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana a ranar Asabar cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamiti na musamman da rarraba kayan tallafi ga jahohi 12 wanda ambaliyar ta lahanta a fadin kasar nan.

Shugaban ya dauki matakin ne biyo bayan karban bayanin ambaliyar ruwan daya faru a shekarar da muke bankwana da ita.

DUBA WANNAN: Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tsere wa hukuma a Katsina

Ambaliya: Buhari ya aika da tallafi Kebbi da wasu jihohi 11
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Garba Shehu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da akayi wa taken 'bayanan ambaliyar ruwa', shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma ce za a sake tura tallafi ga jahohin da ambaliyar ta shafa.

Sanarwar ta kuma ce, "Shugaba Buhari ya karbi rahoton a ranar Asabar kuma ya bada umarnin a kafa kwamiti na musamman don miki tallafin gaggawa ga jihohi 12 da abin ya shafa.

DUBA WANNAN: An kama Sanatan da ake zargi da karkatar da kudin yaki da korona yana boye kudi 'tsakanin mazauninsa' yayin da 'yan sanda suka kai sumame gidansa

"Jihohin da za su karbi bakoncin kwamitin da za su raba tallafin ta hannun Hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) sun hada da: Kebbi, Niger, Kwara, Kogi, Edo, Anambra, Delta, Kano, Jigawa, Rivers, Bayelsa da Adamawa.

"Daga cikin jihohin da kashin farko na tallafin shugaban kasar ya riska akwai; Kebbi, Niger, Kwara, Sokoto, Jigawa da kuma Kaduna.

"Shugaba Buharin ya kuma bayyana alhininsa ga wadanda hadarin ta afkawa, wanda wasu sun rasa iyalansu, gidajensu da kuma muhimman abubuwa na bangaren noma da kiwonsu.

"Shugaban kasar ya kuma bayyana bukatar sa ta haɗa kai tsakanin hukumomin gwamnatin jiha da na tarayya don kawo karshen ambaliyar, da kuma bukatar dogon nazari da kiyaye faruwar wannan iftila'i dama makamantansu."

A wani labarin, wata kotu da ke Mapo, Ibadan a ranar Juma'a ta raba auren shekara 18 tsakanin wani malami, Juel Olutunji da matarsa saboda rashin gamsuwa wurin kwanciyar aure.

Da ya yanke hukunci, Cif Ademola Odunade ya ce an raba auren saboda samun zaman lafiya tsakanin Olutunji da Blessing kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel