Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 54, ta lalata gidaje 30,356 a Kano

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 54, ta lalata gidaje 30,356 a Kano

- Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano, SEMA, ta ce mutane 54 ne suka rasu yayin da gidaje 30,356 suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a bana

- Sakataren hukumar Dakta Saleh Jili ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai a Kano

- Dakta Jili ya ce ambaliyar ruwa ta shafi dukkan kananan hukumomi guda 44 da suke jihar daga watan Yuni zuwa yanzu

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) tace mutum 54 ne suka rasa rayuwakansu yayin da gidaje 30,356 suka lalace saboda ambaliyar ruwa a damunar da ta gabata.

Dakta Saleh Jili, babban sakataren hukumar ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Juma'a.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 54, ta lalata gidaje 30,356 a Kano
Ambaliyar ruwa. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Dakta Jili ya bayyana cewa wannan alkaluma an tattara su ne a kananan hukumomi 44 tsakanin watan Yuni zuwa yanzu.

NAN ya ruwaito cewa hukumar (NiMeT) hadin gwiwa da hukumar (NIHSA) sunyi hasashen cewa kananan hukumomi 20 ne yankin da ambaliyar ruwan ta shafa a bana.

Dakta Jili yace kananan hukomomin da abin ya shafa sune: Rogo, Kabo, Gezawa, Bebeji, Kura, Gwarzo, Shanono, Wudil da Gaya.

Sauran sun hada da ;Danbatta, Bagwai, Rimin Gado, Ungogo, Gwale, Warawa, Tarauni, Nasarawa, Dala, Kumbotso da kuma Kano Munincipal.

"30,356 sun lalace kuma mutum 54 suka rasa rayukansu yayin da 81 suka jikkata saboda ambaliya, guguwa da kuma ruwan sama mai karfi daga watan Yuni zuwa yanzu.

Hukumar tace an samu barkewar gobarar da alkaluma suka nuna takai 2,177, wanda hakan ya janyo lalacewar gonaki 9,127," Dr. Jili ya fada.

KU KARANTA: PSC za ta kori tsaffin jami'an SARS 37 daga aiki

Wadanda annobar ta raba da mahallansu suna ci gaba da samun kulawa tare da iyalansu a wuraren da abin ya shafa.

"Munje inda abin ya shafa domin jajantawa wanda al'amarin ya shafa tare da basu kayayyakin da zasu rage radadin abin da ya same su", Jili ya fada.

Ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da suka raba akwai: buhun buhun siminti, hatsi, kwanukan rufi, barguna, katifu, dama wasu da dama.

Sakataren ya kuma bukaci masu hannu da shuni da kuma ƙungiyoyin tallafawa mara sa karfi da su taimakawa wanda abin ya shafa, sannan yayi kira ga al'umma da su dinga tsaftace magudanan ruwansu don kare afkuwar ambaliyar.

A wani labarin daban, Shugban kasar Kyrgyzstan, Sooronbay Jeenbekov ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Alhamis bayan 'yan kasar sun yi kwanaki suna zanga-zanga.

Shugaba kasar ya ce ya sauka daga mukaminsa ne domin kawo karshen rikicin da ya taso sakamakon tsaikon da aka samu yayin zaben 'yan majalisu a kasar a farkon wannan watan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel