Za'a yi ambaliya a jihohin Najeriya 28 bana - Hukumar NEMA

Za'a yi ambaliya a jihohin Najeriya 28 bana - Hukumar NEMA

Hukumar kai agaji na gaggawa ta kasa watau NEMA ta ce za'ayi ambaliyar ruwan sama a kananan hukumomi 102 na jihohi 28 a fadin tarayya bana.

Dirakta Janar na hukumar, Muhammad Muhammad ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a, 10 ga watan Yuli, 2020.

A jawabin, Diraktan ya ce an yi hasashen hakan ne sakamakon rahoton da ma'aikatar lura da alamuran ruwa a Najeriya (NIHSA) ta saki.

Muhammad Muhammad ya ce karamar hukumar Kaura da Zariya a jihar Kaduna na cikin wadanda ke cikin mumunan hadarin ambaliya.

Ya ce hukumomin agaji su wayar da kan al'umma su kasance a shirye domin Hijra daga muhallansu.

Hakazalika ya shawarci gwamnatoci su shirya yadda zasu dakile wannan ambaliyan idan ya iso.

KU KARANTA: An yi jana'izar dan majalisar Legas, Tunde Buraimoh

Za'a yi ambaliya a jihohin Najeriya 28 bana - Hukumar NEMA
Za'a yi ambaliya a jihohin Najeriya 28 bana - Hukumar NEMA
Asali: Depositphotos

Yace: "Ya kamata a fara kwashe shara, ciyayi, da firanni daga magudanar ruwa da dukkan wuraren da zasu hana tafiyar ruwa,".

A watan Yuni, ambaliyan ya mamaye wasu sassan jihar Legas.

Unguwanni da hakan ya shafa sun hada da Marina, Lekki, Dopemu, Iyana-Ipaja, Egbeda, Ikeja da Ajah.

Ga wasu al'amura da ya dace a kiyaye yayin ruwa mai tsananin karfi.

1. A lokacin da aka fara ambaliya, kada a yi yawo a cikin ruwan. Ruwa mai zurfin inci 6 kacal zai iya tafiya da mutum.

2. Akwai matukar amfani idan aka guji yin wanka a ruwa ko tuka mota a yayin da ake ambaliya. Gara a zauna gida lafiya.

3. Akwai amfani idan aka kiyaye gadoji da kuma ruwa mai tafiya da Sauri. Ruwa mai tafiya zai iya yin awon gaba da jama'a ba tare da an sani ba.

4. Mafi akasarin direbobi basu damuwa da wannan amma yana da matukar hatsari – kada ka kuskura ka tuka abun hawa a yankunan da ked a ambaliyar ruwa.

Idan ambaliyar ruwa ya kai saman motarka, ka yasar da motar sannan hau wajen da ke da tudu sosai idan za ka iya hakan a tsanaki.

5. A kiyaye taba wayar wuta ko wani abu da ke aiki da lantarki idan ruwa ya taba shi.

6. Idan ruwa ya cika gida, a kashe duk wata hanyar wutar lantarki. A kiyaye zama kusa da falwayar wuta a tituna.

7. Zubda shara a kwata ko hanyoyin ruwa na iya kawo toshewar hanyar da ruwa ke gudana. Hakan na iya kawo ambaliyar ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel