Shehu Sani: Duk rana sai Masu garkuwa da mutane sun yi lalata da wadanda su ka tsare

Shehu Sani: Duk rana sai Masu garkuwa da mutane sun yi lalata da wadanda su ka tsare

- Tsohon Sanatan Kaduna ya yi kira a ceto Daliban makarantar da ke garin Afaka

- Sanata Shehu Sani ya ce Miyagu su kan gallazawa wadanda su ka shigo hannu

- ‘Dan siyasar ya ke cewa bayan dukan tsiya, ‘Yan bindiga na lalata da Bayin Allah

Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani ya fito ya na koka wa game da halin da wadanda aka yi garkuwa da su su ke ciki.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ‘yan bindigan su kan yi lalata da duk wadanda tsautsayi ya rutsa da su, su ka fada hannun wadannan miyagun mutanen.

Shehu Sani yake cewa baya ga dukan tsiya, ‘yan bindigan su na amfani da wadanda su ka cafke.

KU KARANTA: An fito da bidiyon Dalibai 39 da aka sace a Kaduna

‘Dan majalisar ya bayyana cewa wannan mummunan lamari ya na auku wa ne a kowace rana, a cewarsa, babu ranar da za ta wuce da ba ayi wannan ta’adi ba.

Ganin har yanzu ba a ceto yaran makarantar da aka sace ba, Sani ya koka da cewa tashin hankalin da daliban nan su ke ciki a halin yanzu, ba zai iya misaltu wa ba.

Fitaccen ‘dan gwagwarmayar da ya shiga siyasa ya bayyana wannan a shafin Twtter, ya na kiran gwamnati ta ceto daliban makarantar gandun noma da aka sace.

“Idan ‘yan bindiga su ka yi ram da mutane, ba ajiye su su ke yi cikin jin dadi har sai an biya kudin fansar su ba. Su na ci masu zarafi ne, su yi amfani da su kullum.”

Shehu Sani: Duk rana sai Masu garkuwa da mutane sun yi lalata da wadanda su ka tsare
Sanata Shehu Sani
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gobara: Minista ta dauki mataki bayan Buhari ya aika tawaga Katsina

Sanata Sani ya cigaba da jawabinsa a dandalin Twitter: “Wani irin yanayi na tashin hankali da ba za iya tunani ba wadannan Bayin Allah su ke shiga a kowace sa’a.”

“Dole ayi duk abin da za ayi domin a ceto ‘daliban makarantun gandun daji.” Inji Shehu Sani.

Kwanakin baya kun ji yadda satar 'daliban makarantar GSS Kagara ya jawo Shehu Sani da Gwamnan Neja su ka yi musayar kalamai a shafukansu na Twitter.

Gwamna Sani Bello ya maida wa tsohon Sanatan martani bayan ya ba shi shawara, gwamnan ya ce zai fi kyau ace Sani ya yi amfani da damar da ya samu a majalisa.

Mun fahimci cewa daga baya Sani Bello ya yi maza, ya goge wannan magana da ya yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel