Satar yaran Kagara ya jawo Shehu Sani da Gwamnan Neja sun yi musayar kalamai a Twitter
- Shehu Sani ya yi kira a tuna da yaron da aka kashe a makarantar Kagara
- Gwamnan Neja ya caccaki Sani, ya ce ina ma ya yi aiki da ya ke Majalisa
- Tsohon Sanatan ya yi martani, ya fadi wasu ayyukan da ya yi a Majalisa
Sanata Shehu Sani ya sake yin magana game da makarantar sakandaren Kagara wanda ‘yan bindiga su ka shiga su ka dauke wasu ‘dalibai da ma’aikata.
Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja ta canza wa makarantar suna, ta sa sunan ‘dalibin da aka kashe a lokacin da ‘yan bindiga su ka kawo masu hari.
Tsohon Sanatan ya yi wannan kira ne a shafinsa na Twitter, amma gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya na da ta-cewa a kan wannan shawara da aka ba shi.
Mai girma Abubakar Sani Bello ya maida wa tsohon Sanatan martani, ya ce zai fi kyau ace ya yi amfani da damar da ya samu a taimakon mutanen da ya wakilta.
KU KARANTA: Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan rikicin Boko Haram
“Nagode Mai girma Shehu Sani, daya daga cikin muradunmu shi ne mu samar da aminci wajen daukar karatu. Amma mutum zai yi tunani za ka yi amfani da basirarka wajen cigaban al’ummar Kaduna ta tsakiya da ka wakilta.”
Daga baya Abubakar Sani Bello ya yi maza ya goge wannan magana da ya yi a dandalin Twitter.
A nan ne Shehu Sani ya maida masa amsa, ya ce: “A shekaru hudu da na yi, na iya gina dakunan shan magani 7 a Kaduna ta tsakiya, da gidaje 9 da mu ka saya wadanda mu ka maida su makaranta da gidajen marayu.”
‘Dan siyasar ya kara da tuna wa gwamnan na Neja cewa akwai bukatar ya gyara wannan makaranta.
KU KARANTA: Ana zargin Darektan NARICT da kabilanci da son kai
A wani bayanin, Sani ya ce ya gyara dakin karatu sannan ya saye littatafai da gafaka, ya tada wurin kwanan yara a wannan makaranta da ya yi karatu a da.
Dazu kun ji Doyin Okupe ya ce wasu dalilai 4 sun tunzuro shi, ya na shirin yin takarar Shugaban Najeriya, daga ciki har da ta'adin 'yan bindiga da ake fuskanta.
Doyin Okupe ya ce ya yi aiki da shugabannin kasa biyu, don haka yake ganin zai iya rike Najeriya, ya maida kasar a kan saiti saboda basira da ilmin da yake da shi.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng