Ba Da Yawun Mu Kake Magana Ba: Dattawan Yarbawa Sun Barranta Kansu Da Sunday Igboho

Ba Da Yawun Mu Kake Magana Ba: Dattawan Yarbawa Sun Barranta Kansu Da Sunday Igboho

- Dattawan yarbawa sun nesanta kansu da yunkurin fitar da yarbawa daga Nigeria da Sunday Igboho ke neman yi

- Kunle Olajide, Sakataren Kungiyar Dattawan Yarbawa ta YCE ne ya bada wannan sanarwar inda ya ce babu wanda ya bawa Igboho damar magana a madadin dukkan yarabawa

- Olajide ya ce tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka Yarbawa ke zaune da sauran kabilu kuma sun bada gagarumin gudunmawa wurin gina kasar

Kunle Olajide, babban sakataren kungiyar Yoruba Council of Elders (YCE) ya ce Sunday Adeyemo, shugaban matasan yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ba ya wakiltan Yarbawa a yunkurinsa na kafa kasar yarbawa.

Igboho a baya bayan nan ya ce Yarbawa sun fice daga Nigeria, inda ya yi kira ga Yarbawa da ke arewa su dawo gida, The Cable ruwaito.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

Da ya ke hira da The Cable a ranar Laraba, Olajide ya ce Nigeria za ta fi karfi idan ta cigaba da zama a matsayinta na kasa guda daya.

Shugabannin Yarabawa sun ce ba su goyon bayan Sunday Igboho
Shugabannin Yarabawa sun ce ba su goyon bayan Sunday Igboho. Hoto: @thecableng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Ya ce Yarbawa sun bada gudunmawa sosai wurin gina Nigeria da hadin kanta don haka babu hikima ta ce za ta fice a kasar a yanzu.

Olajide ya ce: "Wannan ra'ayinsa ne (Igboho) amma halin da muke ciki yanzu hakan ba zai haifar mana alheri ba, kuma dai Yarbawa sun zuba hannun jari mai dimbin yawa wurin hadin kan kasa da gina kasa. Kabilar ba za ta fice daga kasar ba tare da cikakken shiri ba.

"Ban da masaniya kan cewa Yarbawa sun shaida wa wani cewa suna son ficewa daga Nigeria. Don haka wannan ba shawara bace da yarbawa suka yi.

"Duk wanda ya san tarihin Nigeria ya san mun shafe shekaru fiye da 100 tare, tun kafin zuwan turawan Birtaniya akwai Yarbawa da sauran kabilu a sassan Nigeria.

"Wannan ba abinda wani zai iya furtawa bane kawai don kansa. Banbancin kabilu da yawan al'umma shine karfin mu a kasar nan. Rabuwar kai da rarraba kasar ba zai zama alheri gare mu ba."

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel