Hatsarin Jirgin Ruwa: Jami'in Kwastam Ya Mutu Yayin Kokarin Kama Ƴan Smogal

Hatsarin Jirgin Ruwa: Jami'in Kwastam Ya Mutu Yayin Kokarin Kama Ƴan Smogal

- Wani jami'in hukumar Kwastam mai suna Aliyu AA ya riga mu gidan gaskiya a Legas

- Mai magana da yawun hukumar Kwastam, Idaho Sulaiman ya bada sanarwar rasuwar

- Sulaiman ya ce Aliyu AA ya rasu ne sakamakon hatsarin jirgin ruwa yayin da suka fita aiki

Hukumar Yaki da Masu Fasabkwabri, Kwastam, Western Marine Command, WMC, a ranar Laraba ta ce ta rasa daya daga cikin jami'anta sakamakon hatsarin jirgin ruwa a ranar Litinin, rahoton The Nation.

Kakakin hukumar, Idaho Sulaiman ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar a Legas.

Hatsarin Jirgin Ruwa: Jami'in Kwastam Ya Mutu Yayin Kokarin Kama 'Yan Smogal
Hatsarin Jirgin Ruwa: Jami'in Kwastam Ya Mutu Yayin Kokarin Kama 'Yan Smogal. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 6.10 na yammacin ranar 22 ga watan Maris yayin da jami'an hukumar na yankin Akere karkashin Idiroko suka fita sintiri bayan samun bayannan sirri a yankin Vawhe-Isalu.

Suleiman ya ce tawagar karkashin jagorancin Sufeta na Kwastam, Ajayi AS, ta yi hatsarin ne yayin kokarin tare wani jirgin ruwa da ake zargin yana dauke da haramtattun kaya.

"Hatsarin ya yi sanadin rasuwar Mataimakin Sufeta na Kwastam, (AIC) Aliyu AA bayan nutsewa da ya yi a cikin ruwa.

"An gano gawar mamacin a kasan rafin da taimakon mazauna kauyen da ke kusa da ruwan yankin.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Ba Za Su Ajiye Makamai Ba Sai An Basu Tabbacin Babu Abin Da Zai Same Su, Sheikh Gumi

"An kai gawar zuwa babban asibitin Badagry daga bisani aka ajiye a dakin gawarwaki bayan likitoci sun tabbatar ya mutu.

"An dauki gawar a jirgin sama na MAX air zuwa Kano a ranar 23 ga watan Maris bisa umurnin yan uwan mamacin," in ji shi.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel