Okorocha ya yi alkawarin gina Makarantun Almajirai a Katsina, Kano, Yobe, Borno da Zamfara

Okorocha ya yi alkawarin gina Makarantun Almajirai a Katsina, Kano, Yobe, Borno da Zamfara

- Sanata Rochas Okorocha zai ginawa Almajirai makarantun zamani a Arewa

- Za a gina wadannan makarantu ne a Katsina, Bauchi, Yobe, Zamfara da Kano

- Gidauniyar Rochas Foundation ta na kokarin gyara tsarin almajiranci a kasar

- Wadannan makarantun za su hada koyar da karatun boko da ilmin Al’Qurani

A yunkurinsa na shawo kan matsalar da ta ke tattare da almajiranci a Najeriya, Sanata Rochas Okorocha zai gina makarantun tsangaya na zamani.

Jaridar Katsina Post ta rahoto cewa Sanatan na Imo ta yamma zai gina wadannan makarantun ne a wasu jihohi shida na yankin Arewacin kasar nan.

Tsohon gwamnan jihar Imo zai yi wannan kokari ne ta hannun gidauniyarsa ta ‘Rochas foundation’ wanda ta dade ta na irin wannan namijin aiki.

KU KARANTA: Fitattun makarantun ilmi 12 da ake ji da su a birnin Zazzau

Babban jami’in wannan gidauniya kuma tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Alhaji Abdulmalik Mahmud, ya bada sanarwar nan a ranar Litinin.

Abdulmalik Mahmud ya bayyana wannan ne a lokacin da jagoran Tijjaniyya na Afrika, Sheikh Ahmad Tijjani Nyass ya kai masu ziyara a garin Bauchi.

Mahmud ya ce jihohin da za su samu wadannan makarantun almajirai na zamani sun hada da ita kan ta Bauchi da Kano, Katsina, Yobe, Borno, sai Zamfara.

Wadannan makarantu za su hada karantun addini musamman Al-qur’ani da karatun zamani na boko.

KU KARANTA: Boko Haram su na daukar Almajirai, su ba su makamai - Ganduje

Okorocha ya yi alkawarin gina Makarantun Almajirai a Katsina, Kano, Yobe, Borno da Zamfara
Gidauniyar Rochas Okorocha ta na taimakon talakawa
Asali: Facebook

Gidauniyar Rochas Fondation ta ce akwai alaka mai karfi tsakanin jahilicin da ake fama da shi a kasar nan da kuma rashin tsaro da ya dabaibaye al’umma.

A jawabinsa, Sheikh Nyass ya yabi Okorocha, ya yi kira ga sauran masu kudi su yabi wannan Attajiri da banbancin addini bai hana sa bada taimako ba.

Shugabar makarantar Rochas foundation college ta jihar Bauchi, Misis Sarah Johnson, ta bayyana cewa an kafa makarantun ne domin ‘ya ‘yan talakawa.

Kwanakin baya kun ji cewa fitaccen shehin darikar tijjaniyyah na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ja kunnen gwamnoni a kan batun almajiranci.

Da yake karatun tafsirinsa na shekarar bara, Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga gwamnonin yankin Arewacin Najeriya su daina tsangwamar almajirai.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel