Jaruman matan Arewacin kasar nan 3 da su ka shiga Soja, 'Yan Sanda, su ka kai manyan matsayi

Jaruman matan Arewacin kasar nan 3 da su ka shiga Soja, 'Yan Sanda, su ka kai manyan matsayi

A wannan karo, legit.ng Hausa ta tattaro maku jerin wasu daga cikin matan Arewa da su ka yi fice a aikin khaki , su ka taka inda maza su ke taka wa.

Wannan jeri da mu ka kawo ya na kunshe da manyan mata a cikin sojojin kasa, sama, da na ruwa, da jami’an ‘yan sanda wanda su ka kai matakan koli.

Ga wasu daga cikin wadannan bajiman mata da su ka fito daga yankin Arewacin Najeriya:

1. Commodore Jamila Malafa

Commodore Jamila Malafa mutumiyar jihar Adamawa ce. Ita ce soja mace da ta fito daga yankin Arewa da ta kai matsayin da ba a taba samun wanda ta kai a gidan sojan ruwa ba.

Malafa mai shekara 55 ta fito ne daga jihar Adamawa, a Arewa maso gabashin Najeriya. Matsayinta na Commodore ya na kusan daya da Birgediya-Janar a gidan sojan kasa.

A shekarar 1988 ne Jamila Malafa ta shiga aikin sojan ruwa, ta samu lambar yabo na kasa na NPOM a 2019, inda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karrama ta.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram 500 su na daure a gidajen yari - CDS

2. AIG Aishatu Baju

Dr. Aishatu Abubakar Baju DVM, Ph.D ta kai matsayin Mataimakiyar Sufeta-Janar na ‘yan sanda (AIG). Ita ma wannan babbar jami’ar tsaro ta fito ne daga wani kauye a jihar Adamawa.

Bayan zaman ta jami’ar tsaro, Princess Aishatu Baju ta yi karatu har ta samu digirin PhD. A 1995 ta shiga aikin ‘dan sanda, ta zama Kwamishinar ‘yan sanda a 2016 ta na mai shekara 45.

Tsakanin 1987 da 1994 Aisha Baju tayi Digirin farkonta a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fannin likitancin dabbobi. Daga baya ta samu Digirdigir a fannin a jami’ar Plymouth a 2007.

3. Wing Commander Hajara Bashari Umaru

Hajara Bashari Umaru ‘diya ce wurin Marigayi Marafan Birnin Kudu, Kanal Bashari Umaru. Kamar yadda ku ka ji, asalinta mutumiyar garin Birnin Kudu ce a jihar Jigawa.

Wannan jami’ar sojan sama mai shekara 57 a Duniya ta je yakin kasar Kongo, sannan ta yi aiki a Ibadan, Kaduna da wasu wurare a cikin gida bayan shigan ta gidan soja a 1986.

Jaruman matan Arewacin kasar nan 3 da su ka shiga Soja, 'Yan Sanda, su ka kai manyan matsayi
Jaruman matan Arewa Hoto: legit.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojoji za su yi maganin Igbaho da Dokubo Asari

An haifi Wing Commander Hajara Umaru ne a Unguwar Dorayi, jihar Kano a shekarar 1964. Ta yi karatu a firamaren Gwagwarwa da makarantar nan ta St. Louis da ke garin Kano.

4. Group Captain Rahinnatu Garba Talasse

Mace ta karshe ita ce Group Captain Rahinnatu Garba Talasse wanda ta fito daga jihar Gombe. Ita ma ‘yar asalin Arewa maso gabashin Najeriya ce wanda ta kai matsayi na kusan Janar.

A makon nan kun samu rahoto cewa shugaban hafun sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce dakarunsa sun kammala shirin ganin bayan ‘yan bindigan da ke ta tada kafar baya.

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya ce sojoji za su kai wa ‘Yan bindigan harin ayi ta-ta kare, amma ya ce gwamnonin Arewa za su karbi tuban wadanda su ka ajiye makami.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel