Sule da Buni sun yi gargadi game da shirya zanga-zanga a Yobe da Nasarawa

Sule da Buni sun yi gargadi game da shirya zanga-zanga a Yobe da Nasarawa

- Gwamnan Yobe ya bukaci Matasa su yi hattara da shiga zanga-zanga

- Mai Mala Buni ya ce rikicin Boko Haram da jihar ta shiga ya isa haka

- Shi ma Gwamna Abdullahi Sule ya yi irin wannan gargadi a Nasarawa

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira ga matasan jiharsa da na yankin Arewa maso gabashin Najeriya su kaurace wa zanga-zanga.

Mai Mala Buni ya yi kira ga matasansa da su guji biye wa masu zanga-zangar #EndSARS da ake yi a bangarori da jihohi da-dama na Najeriya.

Jaridar The Nation ta ce gwamnan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke kaddamar da wani banki da aka kafa a karkashin tsarin SDG jiya.

KU KARANTA: 'Yan gani kashenin Buhari sun fita zanga-zanga a Fatakwal

Buni ya yi maganan ne a gaban wasu matasa 200 da za su amfana da wannan aiki da aka yi.

Mai girma gwamnan ya ce jihar Yobe ta ga rikicin ta’addancin Boko Haram, don haka ba za ta so ta bar halin zaman lafiyan da ta ke ciki a yau ba.

Shi ma Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya gargadi mutane da su guji shirya zanga-zanga da sunan #EndSARS bayan hukuma ta rusa dakarun.

Gwamnan ya ce masu wannan danyen aiki za su gamu da fushin hukuma a jihar da ya ke mulki.

KU KARANTA: Zanga-zanga: Clinton ta koka da kashen-kashen da aka yi a Legas

Sule da Buni sun yi gargadi game da shirya zanga-zanga a Yobe da Nasarawa
Matasa da ke zanga-zanga Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sule ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wani kwamiti na musamman da gwamnatinsa ta kafa domin ta bincike ta’adin da SARS su ka yi a baya.

Ya ce idan har za ayi zanga-zanga, ya zama daga mutanen gari wadanda su ka san abin da ke faruwa a Nasarawa, ba ayi hayar masu tada rikici ba.

Gwamnatin Legas ta yi magana bayan an budawa Bayin Allah wuta a wajen zanga-zanga. Abin ya yi kamarin da an kashe wasu da aka harba a Lekki.

Sanwo-Olu ya ce ba su taba ganin abu irin haka ba, sannan ya ce lamarin ya fi karfin ikonsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel