Kwankwaso, Tambuwal da Wike su na cikin matsala, da wuya PDP ta ba su tutar 2023

Kwankwaso, Tambuwal da Wike su na cikin matsala, da wuya PDP ta ba su tutar 2023

- Jam’iyyar ta fara shiryawa zaben shugaban kasa na 2023 tun yanzu

- Alamu na nuna za a iya kuma ba Atiku Abubakar takara a jam’iyyar

- APC dai ta doke Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben da aka yi a 2019

Alamu sun fara nuna cewa jam’iyyar adawa ta PDP za ta sake tsaida Alhaji Atiku Abubakar ne a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Jaridar New Telegraph ta fitar da rahoto cewa jam’iyyar PDP ta na ganin cewa idan ta ba tsohon mataimakin shugaban kasar tikiti, za ta iya kai labari.

Wata majiyar cikin gida ta shaida wa Sunday Telegraph cewa tikitin Atiku Abubakar/Peter Obi da aka yi amfani da shi a 2019, zai yi aiki a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: K/Kudu ya kamata PDP ta kai takarar Shugaban kasa - Obaseki

Wasu manyan jam’iyyar hamayyar su na da ra’ayin shugaban kasa Muhammadu Buhari bai lashe zaben 2019, an yi amfani da karfin mulki ne ya zarce.

A zaben 2023, Muhammadu Buhari ba zai iya shiga takara ba, don haka ake ganin takarar Atiku da Obi za ta doke duk wanda APC mai mulki ta tsaida.

Rahoton ya ce sabanin da aka samu tsakanin Atiku da ‘yan siyasar Ibo ya haddasa rashin tsaida matsaya game da yankin da za a ba takara a zaben.

A lokacin da wasu su ke so a sake ba Atiku tikitin PDP, mutanen Kudu maso gabas sun taso da karfinsu, su na ganin lokaci ya yi da za su tsaida ‘dan takara.

KU KARANTA: Buhari zai jagoranci bikin Tinubu Colloquium na shekarar bana

Kwankwaso, Tambuwal da Wike su na cikin matsala, da wuya PDP ta ba su tutar 2023
Alhaji Atiku Abubakar Hoto:www.leadership.ng
Asali: UGC

Idan PDP ta tafi a kan haka, takarar irinsu gwamna Aminu Tambuwal, Bukola Saraki, Nyesom Wike da Rabiu Kwankwaso duk za su fuskanci barazana.

Wasu su na ganin a jingine batun ba Ibo takara sai an samu mulki tukun, sannan hakan zai ba Arewa damar cigaba da mulki, baya ga batun shekarun Atiku.

Kwanakin baya sabon shugaban kungiyar Afenifere watau Cif Ayo Adebanjo, ya tabo batun siyasar 2023 da rade-radin burin takarar Bola Ahmed Tinubu.

Ayo Adebanjo ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai mika ragamar kasar nan ga jagoran APC, Bola Tinubu ba, ya ce yaudarar 'dan siyasar ake yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng