Okowa, Ganduje da wasu gwamnoni 4 da ka iya zama sanatoci a 2023

Okowa, Ganduje da wasu gwamnoni 4 da ka iya zama sanatoci a 2023

- Shekarar 2021 muke amma batun zaɓen 2023 ya karaɗe ko ina a Najeriya

- A 2023, da yawa daga cikin gwamnonin Najeriya na kammala wa'adin mulkinsu karo na biyu

- Tuni dai wasu gwamnonin Najeriya suka fara tattara komatsansu don komawa majalisar dattawa

A yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa, wasu daga cikin gwamnonin Najeriya suna kammala wa'adin mulkinsu karo na biyu kuma suna ƙokarin takarar kujerar majalisar dattawa a jihohinsu.

Komawar gwamnoni majalisa ta zama al'ada a siyasar Najeriya saboda suna kallon majalisar dattawa a matsayin wurin komawa bayan murabus.

Ga wasu, samun kujera a majlisar yana sa a cigaba da damawa dasu a siyasa.

1. Ifeanyi Okowa

Okowa likita ne wanda ya koma siyasa. Yana ɗaya daga cikin taurarin dake haske a PDP. Ɗan siyasa ne nagari kuma akwai yuwuwar ya koma majalisar dattawa a karo na biyu domin ya kasance ɗan majalisa a majalisar dattawa karo na 7.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Kaduna, sun sheke ma'aikacin lafiya da wasu mutum 3

Okowa, Ganduje da wasu gwamnoni 4 da ka iya zama sanatoci a 2023
Okowa, Ganduje da wasu gwamnoni 4 da ka iya zama sanatoci a 2023. Hoto daga Sani Abubakar Bello, Ifeanyi Okowa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Muna nan zuwa kanku, Shugaban sojin Najeriya ga Igboho da Dokubo

2. Ifeanyi Ugwuanyi

Gwamnan jihar Enugu ba sabo bane a siyasar majalisa saboda tsohon ɗan majalisar wakilai ne. Saboda ƙokarinsa ne zai sa jama'arsa su zaɓe shi domin zama a majalisar dattawa.

3. Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu a 2023. Mamallakin digirin digirgir din yayi aiki sosai a fannin ababen more rayuwa a jihar Kano. Akwai yuwuwar gwamnan ya nemi matsuguni a majalisar tarayya.

4. Abubakar Sani Bello

Akwai yuwuwar gwamnan jihar Neja ya koma majalisa a 2023. A bangaren Bello, har yanzu da ƙuruciyarsa kuma yana da biyayya ga magabata masu faɗi a ji a siyasar yankin.

5. Okezie Ikpeazu

Jihar Abia bata taɓa sa'ar da tayi ba na shugaba kamar daga 2015 kuma ta fara ganin sauyi a lamarin mulki. Akwai yuwuwar gwamnan ya koma majalisar dattaaa domin cigaba da ayyukan alherinsa.

6. Udom Emmanuel

Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom yana ɗaya daga cikin gwamnonin da za su ƙare a majalisar dattawa a matsayin sanata a 2023.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar APC, Badaru Abubakar, yace za a yi gagarumin taron jami'iyyar a watan Yuni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai rade-radin dake yawo na cewa za a kara wa'adin mulkin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar kuma za a kara lokacin taron ya wuce watan Yuni.

Amma a wata tattaunawa da manema labarai a sakateriyar jam'iyyar APC da yayi a ranar Talata, Badaru yace kwamitin rikon kwaryan ya shirya domin sauke nauyin dake kansu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng