Sojoji Sun Sheƙe 'Yan Bindiga 11 Bayan Musayar Wuta a Abia

Sojoji Sun Sheƙe 'Yan Bindiga 11 Bayan Musayar Wuta a Abia

- Mutune 11 sun mutu sakamakon artabu tsakanin sojoji da yan bindiga a garin Abia

- Yan bindigan ne suka afkawa sojojin a Ariaria a Abia yayin da suka fito sintiri bayan samun rahotannin sirri

- Wasu majoyoyin sun ce a kalla mutum 16 ne suka rasu amma rundunar soji ta ce mutum 11 ne kuma babu soja da ya mutu

Mutane sun shiga firgici a birnin Aba, cibiyar kasuwanci na jihar Abia a yayin da a kalla mutane 11 suka mutu sakamakon musayar wuta da yan bindiga suka yi da sojoji a daren ranar Talata, Vangaurd ta ruwaito.

An kai wa sojojin hari a shingen da suka kafa ne kwanaki biyu bayan wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe yan sanda uku a Abariba, karamar hukumar Ohafia na jihar.

Sojoji Sun Sheƙe 'Yan Bindiga 11 Bayan Musayar Wuta a Abia
Sojoji Sun Sheƙe 'Yan Bindiga 11 Bayan Musayar Wuta a Abia. Hoto: @Vangaurdngrnews
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Angon Da Ya Auri Matar Da Aka Saka Wa Rana Da Ƙaninsa, Soja, Da Ya Mutu Ya Magantu

Yan bindigan da aka ce sun kai 50 sun afka wa mutanen da ke shataletalen Ariaria a babban titin Enugu/Port harcourt misalin karfe 8.30 na daren ranar Talata suka kai wa sojojin hari.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa kafin yan bindigan su iso, sojojin sun fito sintiri ne sakamakon bayannan sirri da suka samu.

Yayin da wasu rahotanni sun ce mutane 16 aka kashe, cikinsu biyu sojoji, majiya daga rundunar soji ta ce mutane 11 ne suka mutu kuma babu soja a cikinsu.

KU KARANTA: Masu Baburan Adaidaita Sahu Sun Shiga Yajin Aiki a Maiduguri

Wani mazaunin unguwar wanda ke kan hanyarsu zuwa coci a daren ya shaidawa wakilcin majiyar Legit.ng cewa dole ya fasa zuwa inda zai tafi sakamakon musayar wutar da sojojin da yan bindigan suka yi.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel