Yakin da Hukumomin EFCC da ICPC su ka kinkimo, ya raba kan wasu Hadiman Shugaba Buhari

Yakin da Hukumomin EFCC da ICPC su ka kinkimo, ya raba kan wasu Hadiman Shugaba Buhari

- Lauretta Onochie ta ce za a iya kama mutum saboda an ga ya na rayuwar da ta fi karfinsa

- Abokin aikinta, Tolu Ogunlesi, ya kawo hujjar da ta nuna hakan ya sabawa dokar Najeriya

Wata daga cikin masu ba shugaban kasa shawara, Lauretta Onochie, ta yi magana game da dokar da hukumomin yaki da rashin gaskiya su ka shigo da su.

Lauretta Onochie ta fito kafar sada zumunta na Twitter ta na cewa hukumomin EFCC da ICPC za su rika binciken wadanda su ke yin rayuwar da ta fi karfinsu.

Hadimar ta shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana wannan ne a shafin Twitter, ta ce za a rika cafke mutane su yi bayanin yadda su ka samu dukiyarsu.

KU KARANTA: Da gaske Gwamna Ortom ya sheka gudu a jeji - Hadiminsa

Onochie ta ce: “Bibiyar yadda mutane su ke rayuwa ya samu daurin gindi yanzu a dokar Najeriya.”

Ta ce: “Hukumomin yaki da rashin gaskiya za su rika cafke masu yin rayuwar da ta dara karfinsu domin su yi bayanin silar arziki da dukiyar da su ka samu.”

Daga yanzu, jami’an ICPC masu yaki da cin hanci da rashawa za su iya taso keyar mutum, har sai ya fada masu yadda ya samu dukiyar da yake tinkaho da ita.

Wannan ra’ayi ya zo dabam da na wani hadimin shugaban kasar, Tolu Ogunlesi wanda yake cewa jami’an ba su isa su kama mutum saboda yadda yake rayuwa ba.

KU KARANTA: Duk da rade-radin rashin jituwa, Buhari zai halarci bikin Tinubu

Ogunlesi ya ce kotu ta haramta wa EFCC da ICPC damke mutane saboda kurum su na caba wa.

Tolu Ogunlesi ya rubuta a shafinsa na Twitter: “Kotunan Najeriya (har kotun koli) sun zartar da hukunci cewa saba wa hakkin ‘dan kasa ne hukumomin yaki da rashin gaskiya su tambayi mutum ya yi bayanin yadda ya ke rayuwar da ta fi karfin samunsa."

Haka zalika Abokin aikin na Misis Lauretta Onochie ya ce sannan gwamnatin tarayya ba ta da damar da za ta karbi harajin da ya kasance hurumin gwamnonin jihohi.

A ranar Litinin ku ka ji cewa EFCC za ta fara kama masu yin rayuwar da ta fi karfin samunsu.

Jami'an hukumomin EFCC da ICPC za su rika binciken duk wasu 'yan Najeriya masu nuna dukiya a kafafen sada zumunta, domin a rika gano masu mallaka dukiyar haram.

Wannan ya biyo bayan umarnin da sabon shugaban hukumar EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa ya bada na binciken dukiya da duk wasu kadarorin ma'aikatan bankin kasar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng