Babu inda ya kai jihar Kano tsaro a Najeriya, Gwamna Abdullahi Ganduje

Babu inda ya kai jihar Kano tsaro a Najeriya, Gwamna Abdullahi Ganduje

- Ganduje ya bayyana wasu irin matakan da gwamnatinsa ta dauka kan tsaro a Kano

- Ministan tsarin Najeriya, Salihi Magashi, ya ce Najeriya na cikin halin kakanikaye

- A cewar Ganduje, jihar Kano ta fi ko ina zaman lafiya a Najeriya

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a ranar Litinin ya bayyana cewa jihar Kano ta fi kowace jiha tsaro a Najeriya bisa matakan da gwamnatinsa ke dauka.

Ya yi alhinin matsalar rashin tsaro a Najeriya, musamman na karshen makon da ya gabata inda aka kaiwa gwamnan Benue, Samuel Ortom, hari.

The Nation ta rahoto Ganduje ya yi wannan jawabi bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa dake Abuja.

DUBA NAN: Hajji 2021: Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari

Babu inda ya kai jihar Kano tsaro a Najeriya, Gwamna Abdullahi Ganduje
Babu inda ya kai jihar Kano tsaro a Najeriya, Gwamna Abdullahi Ganduje Credit: @GovUmarGanduje
Source: Twitter

DUBA NAN: Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

Yace: "Abinda na sani shine a yau jihar Kano ce jiha mafi lumana a fadin tarayya kuma ba haka kawai bane, lallai akwai matakan tsaron da muke dauka, misali hadin kai tsakanin jami'an tsaro a Kano."

"Mun samar da cibiyar leken asiri; CCTV inda muke kallon abinda ke faruwa cikin birnin Kano, mune masu na'urar bibiyan motoci mafi karfi a Kano."

"A dajin Falgore inda yan bindiga ke zama, muka sam, ba zamu yarda a Kano ba. Mun kafa sansanin horon Soji a dajin saboda kada yan bindiga su zauna."

Ganduje ya kara da cewa a Iyakar Kano da Kaduna, akwai daji a wajen kuma sun kafa wani shirin Ruga, sun tattauna da Fulanin daji, kuma sun amince zasu zauna wajen.

"Mun dauki dukkan wadannan matakai ne don samar da zaman lafiya a Kano," Ganduje ya kara.

A bangare guda, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa abokan aikinsa sun damu a dalilin harin da aka kai wa takwaransu, Samuel Ortom.

Jaridar This Day ta rahoto Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na wannan bayani ne a ranar Litinin, 22 ga watan Maris, 2021, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ganduje ya nuna cewa ya na sa rai kwanan nan za a kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a bangarorin Najeriya.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit

Online view pixel