"Ainihin abinda ya faru tsakanin Gwamnan Benuwai da ‘Yan bindiga, ya yi 1km ya na gudu"

"Ainihin abinda ya faru tsakanin Gwamnan Benuwai da ‘Yan bindiga, ya yi 1km ya na gudu"

- Gwamnan Benuwai ya tabbatar da cewa ‘Yan bindiga sun kai masa hari a cikin jeji

- Hadimin Samuel Ortom ya ce ba kirkirar labarin kanzon-kurege gwamnan ya yi ba

- Terver Akase ya ce Gwamnan ya yi gudun kilomita ne saboda ya bar motarsa a nesa

Gwamnatin jihar Benuwai ta bayyana cewa za ta bada hadin-kai domin jami’an tsaro su binciko wadanda su ka nemi su hallaka gwamna Samuel Ortom.

Gwamnatin Benuwai ta kuma yi karin-haske, ta ce ba a sama kurum aka kirkiro labarin harin da aka kai wa Mai girma Samuel Ortom a ranar Asabar ba.

The Nation ta rahoto babban sakataren yada labaran gwamnan, Terver Akase, ya na bayanin ainihin abin da ya faru da gwamnan a makon da ya wuce.

KU KARANTA: Ganduje: Harin da aka kai wa Ortom abin tada hankali ne

Hadimin ya ce: “Gwamna bai gana da masu bincike ba tukuna. Mu na sa ran zuwansu. Gwamna ya nuna shirinsa na hadu wa da su, za mu ba su goyon-baya.”

“Gwamna Ortom ba kirkiro labarin nan ya yi ba. Shakka babu, an kai masa hari. Jami’an tsaro sun tabbatar an nemi a hallaka gwamnan.” Inji Terver Akase.

A cewar Terver Akase, babu abin da zai sa gwamnan ya nemi suna ta hanyar kirkiro labarin kashe shi.

“Eh, ya yi gudun sama da kilomita daya zuwa inda aka ajiye motocinsa. Inda gonarsa ta ke kusa da yankin kogin Benuwai ne, ba za a iya shiga da mota ba.”

"Ainihin abin da ya faru tsakanin Gwamnan Benuwai da ‘Yan bindiga, ya yi 1km ya na gudu"
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ka da a jefa siyasa a harin da aka kai mani - Ortom

“Saboda haka dole aka je da kafa, a hanyar dawowansu ne aka yi masu sameme. Jami’an tsaron da ke tare da shi sun yi kokari, su ka kare harin da aka kawo.”

“Kwarai, bajintar jami’an tsaron da ke tare da shi ne ya ceci shi a ranar. Mu na gode wa Allah." Akaase ya ce ‘yan bindigan ba su ci karfin jami’an tsaronsa ba.

Akaase ya fito ya yi bayanin ne bayan wasu sun fara karyata rahotonnin, su na cewa ba zai yiwu ace gwamna ya sharara tsawon kilomita guda ya na gudu ba.

Tun jiya kun ji cewa kungiyar Arewa Youth Federation (AYF) ta jefa wa gwamnan jihar Benuwai, Mista Samuel Ortom, kalubale kan harin da ya ce an kai masa.

Arewa Youth Federation ta bukaci gwamna Samuel Ortom ya fito da hujjojin da za su nuna makiyaya Fulani ne su ka kai masa hari, kamar yadda ya ke fada.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng