Sanata Jang ya roki Buhari ya saki tsofaffin Gwamnonin Arewa 2 da aka daure a gidan yari

Sanata Jang ya roki Buhari ya saki tsofaffin Gwamnonin Arewa 2 da aka daure a gidan yari

- Jonah Jang ya fito ya na rokon a fito da Sanata Joshua Dariye da Jolly Nyame

- Sanata Jang ya nemi Gwamnatin Tarayya ta yi wa tsofaffin Gwamnonin afuwa

- Istifanus Gyang da Gabriel Suswam sun goyi bayan wannan kira da Jang ya yi

Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito da wasu tsofaffin abokan tafiyar siyasarsa daga gidan yari.

Hukumar dillacin labarai ta rahoto cewa Sanata Jonah Jang ya fito ya na nema wa tsohon gwamnan jiharsa, Joshua Dariye da kuma Jolly Nyame alfarma.

Jonah Jang mai wakiltar kudancin Filato a majalisar dattawa ya roki gwamnatin Muhammadu Buhari ta fito da wadannan mutane biyu daga cikin gidan kaso.

Rahoton ya ce Sanata Jonah Jang da Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa, Istifanus Gyang, sun yi wannan kira ne ranar Lahadi, 21 ga watan Maris, 2021, a garin Jos.

KU KARANTA: Zaman gidan kurkukun shekara 12 ya ga Jolly Nyame

‘Yan siyasar sun yi kira ga shugaban kasa ya yi amfani da karfin ikonsa, ya yi wa Joshua Dariye lamuni, ganin cewa yanayin lafiyarsa ya na kara tabarbare wa.

Sanatocin su na neman wannan alfarma ne bayan kotun koli ta tabbatar da daurin shekara 10 a kan tsohon gwamnan na jihar Filato a sakamakon kama shi da laifi.

Jang ya kuma roki gwamnatin tarayya ta fito da tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame daga kurkuku.

Sanata Jang yake cewa Rabaren Jolly Nyame ya cancanci gwamnati ta yi masa afuwa domin ya shafe wasu daga cikin shekarun da aka yanke masa a gidan yarin.

Sanata Jang ya roki Buhari ya saki tsofaffin Gwamnonin Arewa 2 da aka daure a gidan yari
Jonah Jang da Muhammadu Buhari

KU KARANTA: Kotun koli ta rage adadin zaman kason da Dariye zai yi

Sanata Gabriel Suswam mai wakiltar yankin jihar Benuwai, ya na tare da abokan aikinsa wajen neman alfarmar, ya nemi Buhari ya tausaya wa tsofaffin gwamnonin.

“Ina tare da su wajen kira ga shugaban kasa ya yi rahama, ya yi wa wadannan mutane biyu afuwa.”

A ranar Talata 12 ga watan Yunin 2018 ne Alkali Adebukola Banjoko ta yanke wa Sanata Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato hukuncin shekaru 14 a gidan yari.

An kama Joshua Dariye ne da laifin almubazaranci da N1.162 biliyan a yayin da ya ke kan mulki.

Baya ga shi, akwai wasu sanatoci da hukumar EFCC ta ke gudanar da bincike a kansu, da ma wadanda aka gurfanar a kotu, daga ciki akwai Stella Oduah da David Mark.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel