Mukabala: Lauya ya janye kara a Kotu, Abduljabbar zai zauna da sauran Malamai

Mukabala: Lauya ya janye kara a Kotu, Abduljabbar zai zauna da sauran Malamai

- Kotu ta amince ayi mukabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

- Alkali ya yanke hukunci ne bayan an janye karar da aka shigar a yau

- Wanda ya bukaci a hana zaman, ya nemi kotu tayi watsi da bukatarsa

Rahotanni su na zuwa mana cewa fito-na-fiton da aka shirya za ayi tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da malaman jihar Kano zai kankama.

Gidan rediyon Freedom ya bayyana cewa Barista Ma'aruf Yakassai ya janye karar da ya shigar gaban Alkali, ya na neman a dakatar da duk wani zama.

Da aka zauna a ranar 22 ga watan Maris, 2021, lauyan da ya tsaya wa Ma'aruf Yakassai watau Lukman Auwalu Abdullah, ya janye duka bukatunsa.

Lukman Auwalu Abdullah ya shaida wa ‘yan jarida cewa ya janye bukatarsa a kotu ne bayan sun yi la’akari da bukatar al’ummar jihar Kano a kan lamarin.

KU KARANTA: Babu hannunmu a hana mukabala - Gwamnatin Kano

Barista Lukman Auwalu Abdullah yake cewa mutane sun nuna sha’awarsu ta ayi wannan zama, don haka su ka hakura da bukatarsu saboda kukan al'umma.

Bayan Ma'aruf Yakassai ya gabatar da bukatarsa ta bakin lauyan da ya tsaya masa, kotu ta amince da rokon na sa, ta bada dama a iya yin wannan mukabala.

Wani ma’aikacin BBC Hausa, ya tabbatar da wannan zance, ya ce Lauyan da ya shigar da kara ya hakura ya janye korafinsa, don haka za ayi zama da shehin malamin.

Wanda ya kai kara, Lukman Auwalu Abdullah ya ce tun farko ya nemi shiga cikin shari'ar ne saboda ya na tuhumar malamin da zargin yi wa musulunci batanci.

Mukabala: Lauya ya janye kara a Kotu, Abduljabbar zai zauna da sauran Malamai
Sheikh Abduljabbar Kabara Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Abduljabbar Kabara ya maka gwamnatin jihar Kano a gaban kotu

Har zuwa yanzu, gwamnatin jihar ba ta yi magana a game da wannan sabon hukunci da kotun majistaren na gidan Murtala da ke garin Kano ya dauka ba.

A ranar wata Juma'a ne Mai Shari'a Muhammad Jibrin ya yanke hukuncin haramta a zauna da Abduljabbar Nasir Kabara bayan an hana shi karantar wa.

A wancan lokaci, gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje ta bakin kwamishinan shari'a, Musa Lawan ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni da Alkalin kotu ya yi.

Duka bangarorin malaman na Kano sun nuna rashin jin dadi a lokacin da aka dakatar da zaman, kowane yake cewa a shirya yake ya zauna, ya kare akidunsa.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel