Kungiyoyin Kudu da Arewa sun bada sharuda 5 na cigaba da zama a dunkulalliyar Najeriya

Kungiyoyin Kudu da Arewa sun bada sharuda 5 na cigaba da zama a dunkulalliyar Najeriya

- Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination ta fara barazanar ballewa

- Kungiyar ta ba gwamnatin tarayya sharuda na cigaba da zama tare da sauran ‘Yan Najeriya

Kungiyar nan ta Nigerian Indigenous Nationalities Alliance for Self-Determination ta mutanen tsakiyar Arewa da yankin Kudu ta yi magana a kan tsarin kasar nan.

NINAS ta gabatar da wasu sharudodi biyar da ta ce dole a cika mata su idan har na so su cigaba da zama tare da ragowar jama’a a cikin dunkulalliyar kasar Najeriya.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, kungiyar ta na ganin cewa ta’adin makiyaya da ake fama da shi ya na kare wa ne kan mutanenta.

KU KARANTA: Ba mu cikin kasar Biyafara - IYC, SWF, PANDEF

Shugabannin kungiyar NINAS sun bayyana sharudan na su ne a wajen wani taro da su ka kira a ranar Laraba, an yi wannan zama ne a New Bodija Ibadan, jihar Oyo.

Farfesa Banji Akintoye a matsayinsa na shugaban kungiyar ta NINAS yake cewa:

1. Gwamnatin tarayya ta bada sanarwa, kuma ta karbi korafin da mutanen Kudu da Arewa maso tsakiya su ke yi a kan tsarin mulki da dokar kasa.

2. Gwamnatin tarayya ta fara kaddamar da shirin watsi da kundin tsarin mulkin 1999, a daina amfani da shi.

3. A bada sanarwar dakatar da duk wani zabe nan gaba a karkashin kundin tsarin mulkin 1999 da ake da-ta-cewa a kai.

Kungiyoyin Kudu da Arewa sun bada sharuda 5 na cigaba da zama a dunkulalliyar Najeriya
Zanga-zanga Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

KU KARANTA: Za a ba Kiristocin Arewa mafaka idan aka kafa Biyafara - Nnamdi Kanu

4. Gwamnati ta gayyaci mutanen Kudu da Arewa maso tsakiya domin a tsara shugabanci, da yadda za a fitar da karbar mulki.

5. A fara shirin da zai kirkiro sabon tsarin mulki ta hanyoyi biyu.

A makon da ya gabata, kun ji cewa tsohon tsageran Neja-Delta, Asari Dokubo ya farka, ya na neman ya dawo da ta’adin fafatukar Biyafara a Najeriya.

Mujaheed Asari Dokubo ya na ikirarin zai kafa kasar Biyafara mai cin gashin kan-ta daga Najeriya.

Asari Dokubo ya ce kungiyar Biafra Customary Government da ya ke jagoranta za ta kafa Gwamnoni da za su karbe Jihohin da ke yankin Kudu.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit

Online view pixel