Sanatoci 8 da kan iya bin sahun Dariye zuwa gidan yari

Sanatoci 8 da kan iya bin sahun Dariye zuwa gidan yari

A ranar Talata 12 ga watan Yuni ne Justice Adebukola Banjoko ta yanke wa Sanata Joshua Dariye, tsohon gwamnan jihar Filato hukuncin shekaru 14 a gidan yari saboda almubazaranci da N1.162 biliyan a yayin da yake gwamna.

Kazalika, Banjoko kuma ta zartas wa tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame hukunci mai kama da wannan bayan an same shi da laifin karkatar da kudaden al'ummar jihar sa.

Baya ga Dariye, akwai wasu sanatoci da hukumar EFCC ke gudanar da bincike a kansu da ma wanda aka gurfanar dasu a kotu, ga wasu daga cikinsu.

1) Danjuma Goje

Tsohon gwamna jihar Gombe kuma Sanata mai ci a yanzu yana fuskantar shari'a a kotun tarayya da ke Gombe inda ake zarginsa da damfarar jihar zunzurutun kudi N 5 biliyan.

An ruwaito cewa Goje ya kirkiri sa hannun akawun majalisar jihar Gombe, Shehu Atiku don karbar bashi don yin ayyuka a jihar amma ya karkatar da kudaden.

2) Abdulaziz Nyako

EFCC ta gurfanar da sanata Abdulaziz Nyako mai wakiltan Adamawa ta tsakiya da mahaifinsa kuma tsohon gwamnan Adamawa, Murtala Nyako inda ake tuhumar su da tare da wasu mutane biyu da laifin satar N15 biliyan daga asusun jihar Adamawa ta hanyar amfani da wasu kamfanoni biyar.

Duk da cewa Abdulaziz Nyako ya yi nasara a shari'ar su na farko da EFCC, akwai wasu manyan tuhume-tuhume a kansa har yanzu.

3) Stella Oduah

Tsohuwar ministan filayen jiragen sama tana daya daga cikin sanatocin da EFCC ke tuhuma, ana zargin ta da hannu cikin bayar da kwangilar N9.4 biliyan don samar da kayayakin tsaro a filayen jiragen sama 22 a sassan Najeriya.

An ruwaito cewa ana mata tambayoyi a kan dalilin da yasa bata gudanar da wasu ayyuka ba a filayen jiragen saman duk da cewa an fitar da kudaden.

Wani kamfani mai zaman kansa, Psybernetix Limited ya shigar da karar Stella Oduah wajen EFCC inda ya yi ikirarin cewa ta kwace wasu kwangila da aka bawa kamfani da mika su ga wasu kamfanonin da basu cancanta ba.

4) David Mark

An ruwaito cewa EFCC na bincike game da zargin damfara na N5.4 biliyan da aka ce David Mark ya yi a lokacin da ya ke shugaban majalisa daga 2007 zuwa 2015.

Ana kuma zarginsa da karban kudade daga Sambo Dasuki duk da cewa har yanzu EFCC bata gurfanar dashi a kotu ba.

5) Godswill Akpabio

EFCC ta fara kama tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom din ne a Oktoban 2015 bayan wani Leo Ekpenyong ya shigar da karar cewa Akpabio ya sace kudaden jihar lokacin da ya ke gwamna.

An kuma sake bincikarsa a Satumban 2017 inda ake zarginsa da bawa wata banki kyautar N1.4 biliyan ba tare da wani dalili ba.

A halin yanzu hukumar na iya waiwayar sa a kowanne lokaci

6) Ike Ekweremadu

Gwamnatin tarayya tana tuhumar mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da laifin zamba da damfara.

Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Okoi Obono-Obla ta shigar da kara kotu inda ta ke bukatar kwace gidaje 22 malakin Ekweremadu wanda bai bayyana a cikin kadarorinsa ba.

Sai dai Ekweremadu ya ce ba bu laifin da ya aikata kuma har yanzu shari'ar na kotu

7) Peter Nwoboshi

Sanata Nwoboshi mai wakiltan Arewacin Delta na fuskantar tuhumar aikata laifuka biyu da suka shafi makirci da karkatar da kudaden al'umma a ta hanyar bayar da kwangilar sama da N6 biliyan ga wasu kamfanoni mallakarsa da abokansa a 2016.

Nwoboshi ya yi kwanaki biyu a gidan yari amma kotu ta bayar da belinsa, an fara shari'ar Nwoboshi a ranar 20 ga watan Yuni a babban kotun Legas inda EFCC ta gabatar da shedu biyu.

8) Bassey Akpan

EFCC ta damke Bassey Akpan mai wakiltan Arewa maso gabashin Akwa Ibom bisa zarginsa da karabar ababen hawa wanda kudinsu ya haura N300 miliyan daga hannun wani dilalin man fetur da ake tuhuma da rashawa mai suna Jide Omokore.

EFCC kuma na bincikar Akpan a kan wasu ayyuka da ya yi lokacin yana kwamishinan kudi a karkashin gwamna Godswill Akpabio.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel