Yadda Ma'aikatan Banki Ke Taimakawa Wajen Almundahana, Barrista Albashir Lawal Likko

Yadda Ma'aikatan Banki Ke Taimakawa Wajen Almundahana, Barrista Albashir Lawal Likko

- Wani lauya mai zaman kansa a Abuja, Barista AlBashir Likko ya yi fallasa kan yadda wasu bankuna ke hadin baki da wadanda ake tuhuma da laifi

- Likko ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke tsokaci kan sabuwar umurnin da shugaban EFCC ya bada na cewa ma'aikatan bankuna su bayyana dukiyoyinsu

- A cewar Likko, akwai wata doka mai suna 'garnishe proceeding' da ke iya bawa kotu damar ta umurci banki ta cire kudi daga asusun wanda ake tuhuma a bawa wanda ya shigar da kara

- Sai dai a cewar Likko, wasu bata gari cikin ma'aikatan bankunan sukan sanar da wanda ake tuhumar, su taya shi boye kudin sannan ya basu wani kaso daga baya

Barista AlBashir Lawal Likko, lauya mai zaman kansa kuma masanin dokokin Nigeria, mazaunin birin tarayya Abuja ya yi fashin baki a kan umurnin da shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayar na cewa dukkan ma'aikatan banki su bayyana dukiyarsu.

A cewar Likko, dokar wacce ya ce ba sabuwa bace za ta taimaka wurin dakile hadin baki da ake samu tsakanin wadanda ake tuhuma da laifi da wasu bata gari cikin ma'aikatan banki.

DUBA WANNAN: Matasan Arewa Sun Bawa Sunday Igboho Wa'adin Awa 72 Ya Kwashe Yarbawa Daga Arewa

Yadda Ma'aikatan Banki Ke Taimakawa Wajen Almundahana, Barrista Albashir Likko
Yadda Ma'aikatan Banki Ke Taimakawa Wajen Almundahana, Barrista Albashir Likko
Source: Twitter

Babban lauyan, a hirar da ya yi da Legit.ng Hausa ya ce akwai wasu ma'aikatan banki da ke taimakawa wadanda ake tuhuma ko zargi wurin boye kudadensu da ke asusun ajiyar bankuna ta yadda idan kotu ta nemi bayani a kan asusun bankunan, sai a ga babu wani kudin kirki a ciki.

Likko ya yi bayanin cewa akwai wata tsarin doka da ake kira 'garnishee proceeding' wacce ke tilasta banki ta ciro kudade daga asusun wanda aka samu da laifi ta biya wanda aka zalunta ko da bada izinin mai asunsun bankin ba.

KU KARANTA: Da Dumi-Duminsa: Jami'an Ƴan Sanda Sun Kwance Bam a Kano

Sai dai abinda ke faruwa a wasu lokutan shine bata garin ma'aikatan bankunan su kan hada baki da mai asusun ya basu wani kaso cikin kudin sai su boye kudaden a wasu wuraren ta yadda za su fadawa kotu cewa ba shi da kudi ballantana a biya bashi ko diyyar da kotu ta ce a biya.

Ya bada misali da cewa, "wannan ya taba faruwa a ranar 1 ga watan Maris ina gaban wani alkali a Apo court 35, an zo an shigar da garnishee, duk bankunan sun zo sun ce babu kudi."

Barrista Likko na ganin wannan dokar za ta taimaka wurin dakile irin wannan hadin bakin idan har an tilastawa ma'aikatan banki bayyana dukiyoyinsu da abinda suka mallaka.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel