Yan bindiga sun kai mumunar hari Kaduna, sun kashe 13, sun kona gidaje 56

Yan bindiga sun kai mumunar hari Kaduna, sun kashe 13, sun kona gidaje 56

- Yan bindiga sun sake kai hari kan al'ummar jihar Kaduna

- Wannan karon basu sace mutane ba, hallaka jama'a sukayi da kuma sace amfanin gonansu

- Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i ya yi alhinin abinda ya faru

Wasu yan bindiga sun wasu hare-hare kananan hukumomi uku - Zango-Kataf, Kauru, da Chikun - a jihar Kaduna inda suka hallaka akalla mutum 13 tare da jigata mutum bakwai.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

A cewarsa, hare-haren yayi sanadiyar mutuwar mutum 13.

Aruwan ya yi bayanin cewa yan bindigan sun fara kai hari kauyen Gora Gan na karamar hukumar Zango-Kataf inda suka kashe wani Irmiya Godwin yayinda yake hanyarsa ta komawa gida daga gona.

Kwamishanan ya kara da cewa a karamar hukumar Kauru, yan bindigan sun hallaka mutum 10, kuma suka jigata 4.

"Gidaje 56 da babura 16 aka kona, hakazalika wajen ajiyan doya," yace.

KU KARANTA: Rikicin Hijabi: Jami'an gwamnati sun balle kofar makaranta yayinda Kiristoci suka hana shiga

Yan bindiga sun kai mumunar hari Kaduna, sun kashe 13, sun kona gidaje 56
Yan bindiga sun kai mumunar hari Kaduna, sun kashe 13, sun kona gidaje 56 Credit: @GovKaduna
Asali: Facebook

DUBA NAN: Wajabcin bayyana dukiyoyin ma’aikatan Banki: Sabon Shugaban EFCC ya yi daidai, Barista AlBashir Likko

Kwamishanan ya bayyana sunayen wadanda aka kashe matsayin Esther Bulus, Maria Bulus (diyar Esther yar shekara guda), Lami Bulus, Aliyu Bulus, Monday Joseph, Geje Abuba, Wakili Filibus, Yakubu Ali, Dije Waziri da Joseph Ibrahim.

Wadanda suka jigata a cewar sune Cecilia Aku, Yakubu Idi, Godiya Saleh, da Moses Adamu,

Ya kara da cewa, "an kai hari kauyen Masaka a karamar hukumar Chikun. An kashe wani Duza Bamaiyi, an jigata mutum biyu. An tura jami'a wajen don dakile yan bindigan."

"Hakazalika yan bindigan sun kashe wani Zakka Pada a Kurmin Kaduna ta karamar hukumar Chikun kuma suka raunata wani Pada Dalle."

A wani labarin kuwa, 'yan sanda a jihar Kano a ranar Juma'a sun kwance wani bam a ƙauyen Aujirawa da ke ƙaramar hukumar Gazawa a jihar kamar yadda TVC ta ruwaito.

Kwamishinan yan sanda, Isma'ila Dikko ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da Kakakin yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna ya fitar a Kano.

Mr Dikko ya ce an sanar da rundunar cewa an gano wani abu da ake zargin bam ne a garin.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel