Rikicin Hijabi: Jami'an gwamnati sun balle kofar makaranta yayinda Kiristoci suka hana shiga
- Rikicin hana sanya hijabi ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Kwara
- Har yanzu gwamnan jihar bai furta kalma guda kan lamarin ba
- A ranar Laraba an yi artabun jefe-jefe tsakanin Musulmai da Kirista
Duk da umurnin gwamnatin jihar Kwara cewa a bude makarantun Mission goma bayan rikicin hana dalibai mata sanya Hijabi, wasu Kiristoci sun garkame kofofin makarantun.
Channels TV ta ruwaito cewa da safiyar Juma'a, Kiristoci sun tare hanyar shiga makarantar suna waka da kalaman nuna rashin amincewa.
Hakazalika an zuba tulin yashi gaban makarantar don hana malamai da dalibai shiga.
Daga baya jami'an tsaro suka balle kofar shiga makarantun karfi da yaji.
Amma a daya daga cikin makaratun, Baptist School, inda aka yi artabu tsakanin Musulmai da Kirista kwanaki biyu da suka gabata, ba a samu hatsaniya ba.
A ranar Alhamis, gwamnattin jihar ta umurci shugabannin makarantun da malaman su koma aji.
Gwamnatin tace akwai bukatar hakan saboda daliban azuzuwan karshe su shiryawa jarabawar karkare karatun sakandare.
Gwamnati ta yi gargadin cewa duk Malamin da yaki hallara a makaranta zai fuskanci fushin hukuma.
Kalli bidiyon:
DUBA NAN: Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa
A bangare guda, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, Sarkin Ilorin kuma shugaban kwamitin masu sarauta na jihar Kwara, ya bukaci musulmi da kirista na jihar su rungumi zaman lafiya.
Sulu-Gambari ya yi wannan rokon ne a Ilorin, ranar Laraba cikin wata sanarwa da kakakinsa Mr AbdulaAzeez Arowona ya fitar.
Sarkin mai sanda mai daraja ta daya ya shawarci mabiya addinan biyu su cigaba da zama lafiya da juna domin samun zaman lafiya da cigaba a jihar.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng