Mu na da hujjojin da ke nuna Atiku da PDP sun doke Buhari a zaben 2019 inji Gwamnan Bauchi

Mu na da hujjojin da ke nuna Atiku da PDP sun doke Buhari a zaben 2019 inji Gwamnan Bauchi

- Bala Mohammed ya hakikance cewa PDP ce ta lashe zaben da aka yi a 2019

- Gwamnan na jihar Bauchi ya ce mutane sun yarda cewa PDP ce ta yi nasara

- Mohammed ya na zargin an yi amfani da INEC da jami’an tsaro an yi magudi

Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed, ya ce jam’iyyar su ta PDP ce asalin wanda ta lashe zaben shugaban kasa na 2019.

Da yake magana da Channels TV a jiya, Bala Abdulqadir Mohammed ya fito ya na cewa APC ta yi amfani da kulle-kulle ne ta samu nasara a kan PDP.

A cewar Sanata Bala Mohammed, jam’iyyar APC mai mulki ta yi amfani da hukumar zabe na kasa watau INEC da kuma jami’an tsaro wajen tafka magudi.

“Abin da ‘yan PDP da mutane duk su ka yi imani shi ne mu ne mu ka ci zabe, amma an doke mu ne saboda magudi, jami’an tsaro da INEC sun yi murdiya.”

KU KARANTA: Akwai yiwuwar jam'iyyar PDP ta sake ba ‘Dan siyasar Arewa tikitin 2023

Ya ce: “Ba mu so mu yi ta raki, mun duba mun gano abin da ya hana mu cin zabe. Mu na da hujjoji barkatai da mu ka gabatar, amma kotu ba ta karba ba.”

“Maganar ita ce dukkanmu ‘yan Najeriya ne, mun san duk wani sako da kwararo na Najeriya. Mun san abin da ya wakana a zaben 2019.” Inji gwamna Bala.

Da yake bada wasu misalai, Bala ya ce: “A irinsu jihar Borno da ake fama da matsalar tsaro, ba a yi zabe ba, amma aka tattaro wasu alkaluma, aka gabatar.”

Gwamnan ya cigaba da cewa: “A wasu jihohin da mu ke da karfi, sai kuma aka yi mana kafa.”

KU KARANTA: Garkame iyakokin da na yi bai yi wani amfani ba - Buhari

Mu na da hujjojin da ke nuna Atiku da PDP sun doke Buhari a zaben 2019 inji Gwamnan Bauchi
Bala ya ce Atiku Abubakar ya zi zabe Hoto: legit.ng
Asali: Original

“Ba wannan gefen kurum mu ke kallo ba, mu na duba kanmu, siyasar cikin gidanmu, da maganar a ba ginshikan al’umma; matasa da mata damar ayi da su.”

Jagoran na PDP ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, 2021, inda ya yi karin haske game da aikin da kwamitinsa ya yi a kan zaben 2019.

A zaben 2023, gwamnan Katsina, Rt. Hon. Aminu Masari ya na ganin cewa maganar gaskiya, ya kamata ace mutanen Kudu su ka fito da 'dan takarar Shugaban kasa.

Da yake bayyana ra'ayinsa, gwamna Aminu Masari ya ce idan har za ayi adalci, to ya kamata ne ‘Yan Kudu su gaji Muhammadu Buhari wanda zai sauka a 2023.

Gwamnan na Katsina ya na tare da takwarorinsa Nasir El-Rufai, Abdullahi Ganduje da Babagana Zulum.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng